An Yankewa Budurwa Daurin Shekaru 2 a Gidan Yari Bisa Zargin Wallafa Hoto Babu Dankwali
- Wata budurwa ta fuskanci daurin shekaru biyu a gidan gyaran hali bayan wallafa hotonta babu dankwali a kasar Iran
- Budurwar mai suna Zeinab Khenyab wacce ke da shagon siyar da kayayyaki ta jawo kace-nace kan abin da ta aikata
- A dokar kasar an bayyana cewa dole ko wace mace daga kasar ko ketare Musulma ko sabanin haka ta saka dankwali a ko wane lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tehran, Iran – Wata budurwa ta shiga matsala bayan an yanke mata hukuncin shekaru biyu a gidan yari kan zargin wallafa hoto babu dankwali.
Budurwar mai suna Zeinab Khenyab wacce ke da shagon siyar da kayayyaki ta jawo kace-nace kan abin da ta aikata, cewar Punch.
Wane hukunci aka yanke wa budurwar?
A watan Disamba har ila yau, an daure ta watanni uku kan zargin yada farfaganda kan kasar ta Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar wacce ta fito daga yankin Kudu maso Yammacin kasar ta dauki hankulan mutane bayan hukumomi sun rufe shagonta.
Idan ba a mantaba a watan Satumbar 2022, mutuwar wata budurwa Jina Amini ya jawo zanga-zangar da ba a taba ganin irin ta ba a tarihin kasar.
A dokar kasar Iran tun 1979 ta bayyana cewa dole ko wace mace daga kasar ko ketare Musulma ko sabanin haka ta saka dankwali a ko wane lokaci.
Mene dokar Iran ke cewa kan mata?
Duk wata mace da aka gani babu dankwali ko hijabi a cikin jama’a za ta fuskanci daurin mafi karanci watanni biyu a gidan kaso, cewar Radio Liberty.
Har ila yau, bayan daurin za ta iya fuskantar biyan kudin tara har dala 25 wanda hakan zai rage yawan aikata laifin a fadin kasar.
Akalla mata 30 aka kama a kasar tun a watan Disambar da ta gabata kan zargin cire dankwali a cikin jama’a.
Aikata hakan babban laifi ne a kasar Iran wanda ta aikata za ta fuskanci mummunan hukunci, cewar PM News.
Faransa ta haramta sanya hijabi
A wani labarin, Kasar Faransa ta amince da dokar hana dalibai mata Musulmai sanya hijabi a makarantu.
Wannan na zuwa ne yayin da kasar ke kokarin rarrabe maganar addini da ilimi ko harkokin rayuwa.
Asali: Legit.ng