Shugaban Kasa Ya Fadi Irin Mummunan Hukunci da Ya Kamata a Yi Kan ’Yan Luwadi, Ya Gargadi Turai

Shugaban Kasa Ya Fadi Irin Mummunan Hukunci da Ya Kamata a Yi Kan ’Yan Luwadi, Ya Gargadi Turai

  • Shugaban kasar Burundi ya ja layi kan masu luwadi da auren jinsi inda ya bukaci daukar mummunan mataki a kansu
  • Evariste Ndayishimiye ya bayyana ce wa duk wanda aka kama a Burundi ya kamata a jefe shi a filin wasa
  • Evariste ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bujumbura, Burundi – Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya bayyana matakin da ya kamata a rinka dauka kan ‘yan luwadi.

Evariste ya ce kamata ya yi a rinka jefe su da su da masu auren jinsi inda ya ce hakan ba wani laifi ba ne.

Kara karanta wannan

Kano: An kama wani matashin da ya sace yaro dan shekara 3, an gano alakarsu

Shugaban kasa ya bukaci a jefe 'yan luwadi har sai sun mutu
Shugaban Burundi ya nuna bacin ransa kan masu aikata luwadi a kasar. Hoto: Evariste Ndayishimiye.
Asali: Facebook

Mene shugaban Burundi ke cewa kan 'yan luwadi?

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kararsa ba ta bukatar duk wani taimako daga kasashen Yamma a kokarin kakaba musu sharadin luwadi da madigo.

Har ila yau, shugaban ya ja aya a cikin littafin Inijla inda ya ce Ubagiji ya haramta neman jinsi kwata-kwata.

Ndayishimiye kara da cewa kararsa bata bukatar fara tattauna magana kan ‘yan luwadi da masu auren jinsi.

Ya ce:

“Duk wanda muka gani a Burundi, ku dauke shi a kai shi filin wasa a jefe shi, hakan bai zama laifi ba.
“Idan mutum na bukatar shaidan, to ya je can ya yi rayuwa a irin kasashen da suka dauki wannan dabi’a, ya tsaya a can kada ya kawo ta nan.”

Wane mataki aka dauka kan 'yan luwadi a Burundi?

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Ya ce luwadi da madigo hanya ce a bayyane tsakanin hanyar gaskiya ta ubangiji da kuma hanyar bata ta shaidan.

Burundi na daga cikin kasashen Afirka da suka haramta luwadi wanda hakan ya sa aka sanya hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.

An yanke wa mutane bakwai hukuncin zama a gidan yari a watan Agusta bayan kotu ta kama su da laifin laifin aikata neman jinsi.

An kama 'yan luwadi 100

Kun ji cewa, Rundunar 'yan sanda ta kama wasu matasa da ke shirin auren jinsi a jihar Delta.

Rundunar ta bayyana haka ne a shafinta na X a ranar 28 ga watan Agustar shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.