Rundunar Sojoji Sun Yi Yunkurin Juyin Mulki A Burkina Faso

Rundunar Sojoji Sun Yi Yunkurin Juyin Mulki A Burkina Faso

  • Sojin da ke mulki a Burkina Faso sun sanar da yunkurin juyin mulki a jiya Laraba da wasu sojoji su ka yi
  • Sojin sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa inda su ka ce an kama sojoji hudu kan zargin cin amanar kasa
  • Kyaftin Ibrahim Traore ya kwace mulkin ne a hannun sojoji a ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 2022

Burkina Faso – Sojojin da ke mulki a kasar Burkina Faso sun sanar da yunkurin juyin mulki.

Sojojin su ka ce sun dakile yunkurin ne da wani bangare na soji su ka yi shirin yi a jiya Laraba.

Sojin Burkina Faso sun dakile yunkurin juyin mulki
An Yi Yunkurin Juyin Mulki A Burkina Faso. Hoto: Ibrahim Traore.
Asali: AFP

Yaushe aka yi yunkurin juyin mulki a Burkina Faso?

Sojin sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa inda su ka ce sojin na kokarin jefa kasar cikin mummunan hali.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta cinye ango, amarya da bakin biki 100 ana tsaka da shagalin aure

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar ta ce:

“Wasu na da mummunan nufi na kai farmaki kan hukumomin kasar da kuma jefa ta cikin mummunan hali, bincike zai tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.
“Jami’an soji da ke da hannu cikin wannan juyin mulki duk an kama su," cewar kakakin sojin, Rimtalba Jean Emmanuel.

Sojojin da ke mulki a Burkina Faso sun karbi mulkin ne ta hanyar kifar da gwamnatin soji a 2022 da ke mulkin kasar kafin su ma su fuskanci hakan.

Kyaftin Ibrahim Traore wanda shi ke jagorantar sojin ya kwace mulkin ne a ranar 30 ga watan Satumbar 2022 wanda shi ne juyin mulki na biyu cikin watanni takwas.

Meye sojin Burkina Faso su ka ce kan juyin mulkin?

Sojin sun sanar da cewa za su yi bayani kan wannan yunkurin juyin mulkin inda su ka ce abin takaici ne sojin da su ka yi alkawarin kare kasa za su aikata haka.

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

Rundunar ta ce an kama sojoji hudu kan zargin juyin mulkin yayin da biyu su ka tsere, cewar Daily Trust.

Sanarwar ta kara da cewa rundunar sojin kasar za ta kaddamar da kwakkwaran bincike don tabbatar da yanke hukunci kan ma su son kawo cikas ga kasar.

Sanarwar ta ce:

"Abin takaici ne yadda sojojin da su ka yi alkawarin kare martabar kasar Burkina Faso za su aikata hakan ga mutanen da su ka zabi 'yanci don gujewa bauta na 'yan ta'adda."

Sojin da ke mulki a yanzu sun kifar da gwamnati ne a 2022 bayan rashin tsaro ya yi kamari a kasar, cewar BBC.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan ta'adda da ke da alaka da Al Qaeda sun tarwatsa Burkina Faso da sauran makwabtanta.

Daga shekarar 2022 zuwa yanzu, an samu juyin mulki bakwai a Nahiyar Afirka gaba daya.

An kifar da gwamnatin Ali Bongo

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Rundunar Soji Ta Yi Ajalin Kasurgumin Kwamandan Boko Haram, Ari Ghana, Da Wasu Mutum 5

A wani labarin, sojoji a kasar Gabon sun kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo makwanni kadan bayan an kifar Mohamed Bazoum.

Bongo ya shafe shekaru da dama ya na mulkin kasar bayan rasuwar mahaifinsa, Omar Bongo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.