China Ta Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Malamar Musulunci A Yankin Uyghur
- Akarshe kasar China ta yanke hukunci kan babbar malamar Musulman yankin Uyghur marasa rinjaye a kasar
- Rahile Davut ta kasance malamar Jami’a kuma mai fafutukar ganin jama’ar Uygur sun samu adalci ganin yadda ake gallaza musu
- Kasar China ta yanke mata hukuncin daurin rai da rai kan zargin yin barazana da kuma barazana ga tsaron kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Beijing, China - Kasar China ta yanke hukunci kan malamar addinin Musulunci a Uyghur bisa zargin barazana da tsorata kasa.
Rahila Davut mai shekaru 57 wacce ke koyarwa a jami’ar Xinjiang, an yanke mata hukuncin daurin rai a rai.
Meye China ke zargin Davut da shi kan Uyghur?
Ana zargin kasar China da kamawa tare da daure mutanen Uyghur tare da muzanta musu wurin dakile haihuwa da kuma yada al’adunsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na zargin wasu masu rike da mukaman gwamnati da kisan kiyashi kan mutanen Uyghur.
Har ila yau, kasar China ta musanta zarge-zargen da ake mata inda ta ce Davut ta daukaka kara kuma ba ta ci nasara ba.
Wata kungiya Dui Hua ta sanar cewa malamar Musuluncin ta yi rashin nasara a kotu bayan yanke mata hukunci a shekarar 2018, cewar VOA.
Sanarwar ta ce:
“Wannan shi ne karon farko da gwamnatin kasar China ta tabbatar da daurin rai da rai ga wani mutum.”
Yayin da gwamnatin China ba ta ce komai game da hakan ba bayan an bukaci ta yi martani kan hukuncin da ta yanken.
Wane hukunci China ta yanke kan malamar Uyghur?
Ana zargin Davut da ta da tarzoma inda aka kama ta tun a watan Disambar shekarar 2017, cewar The Guardian.
Ana zargin kasar China da ta ke hakkin dan Adam musamman Musulman yankin Uyghur da ba su da rinjaye wanda kullum kasar ke musawa.
Yankin Uyghur dai na fama da kisan kiyashi daga kasar China wanda kungiyar kare hakkin dan Adam ke ganin ana musguna musu saboda rashin rinjaye da su ke da shi.
Ana zargin China da dasa na'ura kan kabilar Uyghur
A wani labarin, rahotanni sun tabbatar da cewa ana zargin kasar China na dasa na'ura don ganin halin da kabilar Uyghur ke ciki.
Wani masanin kimiyya ya bayyana cewa an dasa na'urorin ne don sanin yanayin bakin ciki ko tunani da kabilar ke yi.
Asali: Legit.ng