An Gano Yadda Kasar China Ke Dasa Na'urori Kan Musulman Kabilar Uyghur

An Gano Yadda Kasar China Ke Dasa Na'urori Kan Musulman Kabilar Uyghur

- Wani bincike ya bayyana yadda kasar China ta ke amfani da wasu na'urori don sanin fushin musulmai

- An dasa wasu na'urori a yankunan kabilar Uyghur don gano yanayin bacin ransu da damuwarsu

- Kasashe da dama sun nunawa kasar China yatsa kan azabtar da kablibar Uyghur wadanda da dama musulmai ne

A wani bincike da aka gudanar, an bayyana cewa ana gwada wata na'ura da aka rika sakawa a jikin Musulmai 'yan kabilar Uyghur domin gano yanayin bacin rai, kawa-zuci ko damuwarsu.

Wakilin BBC ya ce wani injiniyan manhajar na'ura wanda ya nemi a boye sunansa ya fadi cewa shi ya dasa na'urorin a ofishin 'yan sanda wadanda suke gano abin da mutum ke ji ko kuma yake tunani.

Ya ce ana amfani da na'urar wadda take gano sauye-sauye a jikin dan Adam wajen tantance laifin wanda ke tsare idan babu wata shaidar da ta nuna ya aikata laifi.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya Na Bukatar 'Yan Siyasa Masu Hankali, Gwajin Shan Kwayoyi Ya Zama Dole, NDLEA

An Gano Yadda Kasar China Ke Dasa Na'urori Kan Musulmain Kabilar Uyghur
An Gano Yadda Kasar China Ke Dasa Na'urori Kan Musulmain Kabilar Uyghur Hoto: pri.org
Asali: UGC

Hukumomin China ba su amsa tambayoyin da aka yi musu game da na'urar ba.

Yankin Xinjiang yana da 'yan kabilar Uyghurs marasa rinjaye miliyan 12, wadanda akasarinsu Musulmi ne. Jama'a a cikin lardin suna cikin sa ido na yau da kullum.

Yankin kuma ya kasance gida ne na "cibiyoyin sake ilmantarwa" da kasar China ta yi mai cike da cece-kuce, wanda kungiyoyin kare hakkin bil-adama suka kira da sansanonin tsaro masu tsauri, inda aka kiyasta cewa an tsare mutane sama da miliyan guda.

A kwanakin baya, Amurka, Jamus da Birtaniyya sun yi arangama da China a Majalisar Dinkin Duniya kan yadda take azabtar da kabilar Uighur da mutane daga sauran yankunan da galibinsu Musulmai ne a Xinjiang, Aljazeera ta ruwaito.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Ci Bashin Da Ya Fi Karfin Kaduna, Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP

A wani labarin, Kwamitin Jagorancin Shugaban Kasa (PSC) kan cutar Korona ya fitar da sunayen matafiya 90 da ya ayyana a matsayin ‘Mutanen da ake nema, saboda gujewa kebewar kwanaki bakwai, PM News ta ruwaito.

Kebewa ya zama tilas ga mutanen da suka zo daga kasashe masu tsanani, kamar su Brazil, Indiya da Turkiya, inda ake da yawaitar cutar Korona.

Shugaban kwamitin kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce wadanda suka yi kuskuren sun hada da ’yan Najeriya 63 da 'yan kasashen waje 27.

Asali: Legit.ng

Online view pixel