Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Dokar Korona

Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Dokar Korona

- Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen wasu mutanen da take zargi da saba dokar kebe ta Korona

- An fitar da jerin mutane 90 da suka shigo daga kasashen waje zuwa Najeriya kuma suka ki kebe kansu

- Gwamnati ta ce mutane masu hadari, don haka mutane su kula, an kuma kiraye su da su mika kansu asibiti

Kwamitin Jagorancin Shugaban Kasa (PSC) kan cutar Korona ya fitar da sunayen matafiya 90 da ya ayyana a matsayin ‘Mutanen da ake nema, saboda gujewa kebewar kwanaki bakwai, PM News ta ruwaito.

Kebewa ya zama tilas ga mutanen da suka zo daga kasashe masu tsanani, kamar su Brazil, Indiya da Turkiya, inda ake da yawaitar cutar Korona.

Shugaban kwamitin kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce wadanda suka yi kuskuren sun hada da ’yan Najeriya 63 da 'yan kasashen waje 27.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 3, Sun Fatattaki Kauyuka 8 a Sakkwato

Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Kodar Korona
Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Kodar Korona Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Matafiyan da abin ya shafa, an ce sun iso Najeriya ne daga Brazil, Indiya da Turkiya tsakanin 8 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Mayu na wannan shekarar ta filayen jirgin saman Legas da Abuja, inji TheCable.

Mustapha ya shawarci 'yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan da irin wadannan mutanen, yana mai cewa hakan na da hadari ga lafiyar al'umma.

Ya roki wadanda ake neman da su mika kansu ga ma’aikatun lafiya na jiha mafi kusa cikin awanni 48 masu zuwa domin tantance su.

Ya bukace su da su kira Ma'aikatar Lafiya ta wadannan lambobi 08036134672 ko 08032461990 don neman karin bayani.

Duba cikakken jerin sunayen:

Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Kodar Korona
Jerin Sunayen Mutane 90 da Gwamnati Ke Nema Ruwa a Jallo Saboda Saba Kodar Korona Hoto: pmnewsnigeria.com

KU KARANTA: Cece-Kuce Yayin da Wasu Gwamnoni Suka Halarci Biki Maimakon Jana'izar Janar Attahiru

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta ce ba zata kara farashin famfo na man fetur cikin gaggawa ba, a cewar Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Daily Trust ta ruwaito.

Sylva ya fadi haka ne yayin da yake martani kan shawarar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) cewa farashin mai ya kamata ya kasance tsakanin N380 da N408.5 kowace lita.

Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a ranar Laraba 20 ga watan Mayu ta shawarci gwamnatin tarayya cewa ta kara farashin famfo na man fetur tare da cire tallafinsa ba tare da bata lokaci ba, Arise Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel