China Ta Rage Yawan Basukan Da Ta Ke Bai Wa Najeriya Da Sauran Kasashe Saboda Saba Doka

China Ta Rage Yawan Basukan Da Ta Ke Bai Wa Najeriya Da Sauran Kasashe Saboda Saba Doka

  • Yayin da kasashen Nahiyar Afirka ke shiga matsin tattalin arziki, kasar Sin ta rage yawan kudaden bashin da ta ke ba su
  • Hukumar Kula da Basuka a Najeriya (DMO) ta bayyana cewa yawan kudin da ake bin Najeriya ya karu daga Naira tiriliyan 49.8 zuwa 87.379
  • Kasar Sin ta rage yawan ba da basukan ne ganin yadda ita ma ta shiga matsin tattalin arziki yayin da kasashen su ka gagara biya

FCT, Abuja – Yawan bashin da kasar Sin da ta ke bai wa Nahiyar Afirka ya ragu zuwa Dala biliyan daya a shekarar da ta wuce mafi karanci kenan cikin shekaru 20.

Wannan na zuwa ne yayin da mafi yawan kasashen Nahiyar Afirka su ka gagara cika umarnin biyan bashin, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Wike Ya Rusa Shahararriyar Kasuwar Kilishi a Abuja, Ya Fadi Dalili

China ta rage yawan basukan da ta ke bai wa Najeriya
China Ta Rage Yawan Basukan da Ta Ke Bai Wa Najeriya. Hoto: FG, BBC.
Asali: UGC

Meye kasar China ke cewa kan Najeriya da kasashe?

Wani bayani daga Jami’ar Boston ya bayyana cewa Sin ta rage kudaden ne yayin da kasashen Afirka ke fama da matsalolin bashi inda Sin ke fama da matsalar kudi a bangarenta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kasar Sin, XI Jinping ya himmatau wurin samar da lamuni ga kasasehn Nahiyar Afirka da sauran taimako ta bangarori da dama.

Sin ta bai wa kasashen Nahiyar Afirka akalla Dala biliyan 17 daga shekarar 2000 zuwa 2022.

Amma daga bisani yawan ba da lamunin ya ragu a shekarar 2016, yayin da a shekarar 2021 kasar ta ba da mafi karancin bashin da bai wuce Dala miliyan 994 ba.

Me ya jawo cikas a bashin da China ke bai wa Najeriya?

An damu tsaiko tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 saboda bullar cutar ‘Korona’ da ta addabi duniya baki daya, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Da gaske sojoji sun kwace mulki a kasar Kongo? Mun binciko muku gaskiyar batu

Mafi yawan kasashen Nahiyar Afirka na jin dadin basukan da kasar Sin ke ba su da kuma zuba hannun jari a bangarori da dama.

Amma kasashen Yamma na kushe tsarin inda su ka zargi Sin da karawa matsiyatan kasashen Afirka nauyin bashi.

Hukumar Kula da Basuka a Najeriya (DMO) ta bayyana cewa yawan kudin da ake bin Najeriya ya karu daga Naira tiriliyan 49.8 zuwa 87.379 a watan Yuni na shekarar 2023.

inubu ya gaza biyan bashi har Tiriliyan 87

A wani labarin, yayin da ake bin Najeriya Naira tiriliyan 87, Tinubu ya gaza biyan China da sauran kasashe.

A kwanakin baya Tinubu ya sha alwashin rage yawan ciwo bashi da kasar ke yi daga kasashen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.