Girgizar Kasar Morocco: Yawan Mutanen Da Suka Rasu Ya Karu Zuwa 2,497

Girgizar Kasar Morocco: Yawan Mutanen Da Suka Rasu Ya Karu Zuwa 2,497

  • Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasar da aka yi a Morocco ya karu
  • An bayyana cewa a yanzu haka mutane kusan 2500 ne aka samu tabbacin mutuwarsu a ibtila'in
  • Ofishin harkokin gida na ƙasar ta Morocco ya kuma bayyana cewa mutane da dama ne suka samu raunuka sakamakon girgizar ƙasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rabat, ƙasar Morocco - Adadin mutanen da suka rasu a sanadiyyar girgizar ƙasa a Morocco ya kai 2,497 kamar yadda ministan harkokin cikin gida na ƙasar ya bayyana.

Haka nan ma ma'aikatar cikin gidan ta tabbatar da cewa mutane aƙalla 2,476 ne kuma suka jikkata sanadiyyar girgizar ƙasar kamar yadda NDTV World ta ruwaito.

Yawan mutanen da girgizar ƙasa ta halaka a Morocco ya kai 2,497
Adadin mutanen da suka rasu sakamakon girgizar ƙasa a Morocco ya ƙaru zuwa 2,497. Hoto: Hoto: Reuters, NEB Result and News
Asali: Facebook

Yawan barnar da girgizar ƙasar Morocco ta yi

A ranar Juma'a da ta gabata ne dai aka samu girgizar ƙasa mai ƙarfi, wacce ta auku da misalin ƙarfe 11 na daren ranar, inda a take aka gano gawarwakin mutane 632.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 Sace Wasu Mutane Masu Yawa a Arewacin Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai an ci gaba da tono mutanen da baraguzan gine-gine suka danne, inda ya zuwa yanzu da ake ci gaba da bincike, aka iya gano mutane 2,497 da suka mutu.

Mahukuntan Morocco sun ba da hutun kwanaki uku a ɗaukacin ƙasar domin nuna alhini da jimamin mutanen da suka rasa rayukan na su.

Girgizar ƙasar wacce aka shafe shekaru masu yawa ba a yi irinta ba, za a ɗauki lokaci mai tsayi kafin a iya gyara ɓarnar da ta yi kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar ta bayyana.

Duka abokan aikina sun rasa wani na su a girgizar ƙasar

Wani mai suna Mohcine Fala da yake aiki a wani Otal ya bayyana cewa duka abokan aikinsa sun rasa wani ɗan uwa na sa a girgizar ƙasar da ta faru.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rayukan Mutane Da Dama Sun Salwanta a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Arewacin Najeriya

Ya shaidawa BBC Africa cewa mutane takwas ne suka rasu a gidan wata daga cikin abokan aikin na sa, ciki kuwa har da ɗanta mai shekaru bakwai a duniya.

Ya ƙara da cewa abin akwai tashin hankali a yayinda mutum ya fahimci cewa baraguzan gine-gine sun binne 'yan uwansa.

Girgizar ƙasa ta halaka sama da mutane 44,000 a Turkiyya

Legit Hausa a farko-farkon shekarar nan ta 2023 ta yi rahoto kan wata mummunar girgizar ƙasa da aka yi a ƙasashen Turkiyya da kuma Syria.

An bayyana cewa sama da mutane 44,000 ne suka rasa rayukansu a sakamakon girgizar ƙasar mai tsananin gaske da ta wakana a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng