Kotun Kolin Faransa Ta Amince Da Dokar Hana Sanya Hijabi Ga Mata Musulmai A Makarantu

Kotun Kolin Faransa Ta Amince Da Dokar Hana Sanya Hijabi Ga Mata Musulmai A Makarantu

  • Babbar kotun kolin Faransa ta yanke hukunci kan dokar hana sanya hijabi ga dalibai mata Musulmai
  • Wannan na zuwa ne bayan makarantu a Faransa sun kora dalibai kusan 300 kan karya dokar
  • Wannan lamari ya jawo cece-kuce wanda ya jawo zazzafan muhawara a tsakanin 'yan siyasar kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Paris, Faransa - Kotun Koli da ke kasar Faransa ta yanke hukunci kan karar da kungiyar Musulmai ta shigar kan dokar hana sanya hijabi ga dalibai.

Kungiyoyin Musulmai na Action for the Rights of Muslim da Council of the Muslim Faith sun shigar da kara don kalubalantar dokar.

Kotun kolin Faransa ta yanke hukunci
Kotun Kolin Faransa Ta Yanke Hukunci Kan Dokar Sanya Hijabi A Makarantu. Hoto: Emmanuel Macron.
Asali: Twitter

Meye kotun Faransa ta ce kan dokar sanya hijabi?

Sai dai kotun ta tabbatar da sabuwar dokar da gwamnatin ta saka na haramtawa mata Musulmi sanya hijabi a manyan makarantu.

Kara karanta wannan

Lauyan Atiku Ya Fara Nuna Matakin da Za a Dauka Bayan Nasarar APC a Kotu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan ba a mantaba Faransa ta kafa dokar ce don raba lamurran hukumomi da addini, cewar Al Jazeera.

Ta ce dokar za ta hana fayyace wane addini mutum ya ke a makaranta wanda zai taimaka wurin rage cin zarafin dan Adam.

Kungiyoyin Musulmai da sauran daidaikun mutane sun soki wannan doka da cewa cin zarafi ne.

Da kotun ke yanke hukunci, ta ce ba za ta iya amincewa da bukatarsu ba don haka ta tabbatar da dokar, CNN ta tattaro.

Wasu karin dokoki a Faransa

Har ila yau, Faransa ta sanya doka har a filayen wasa ma, inda ta ce bai kamata mata su rika rufe jikinsu ba don jefa fargaba a zukatan ’yan wasa.

Hukuncin kotun na zuwa ne bayan korar wasu dalibai kusan 300 a makarantu saboda karya dokar hana sanya hijabin.

Kara karanta wannan

"Babu Dawowa Baya", Kashim Shettima Ya Tona Asirin Shirin Masu Handame Kudaden Tallafi, Ya Tura Gargadi

Bayan dokar hana sanya hijabi a makarantu, Faransa ta kuma haramta hakan a filayen wasa inda mata Musulmai ke rufe jikinsu.

A cewar dokar, bai kamata a tallata addini a filayen wasanni ba don hakan na iya kawo tsaiko da kuma rashin sakewa ga 'yan wasa.

Wata kungiyar mata Musulmai 'yan wasan kwallon kafa ta shigar da kara amma har yanzu kotu ba ta yanke hukunci a kai ba.

Makarantu A Faransa Sun Kori Dalibai

A wani labarin, bayan saba dokar hana sanya hijabi a makarantu, dalibai da dama sun koma gidajensu.

Wannan na zuwa ne bayan kasar Faransa ta kudiri aniyar raba addini da lamuran hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.