Zanga-zanga kan hijabi na bazuwa a kasar Farisa ta masu Shi'a

Zanga-zanga kan hijabi na bazuwa a kasar Farisa ta masu Shi'a

- Mata a Iran na ta cire hijabi domin a cewarsu sun gaji da 'qaqabe'

- A sharia dai ta Islama, dole mace baliga ta sanya hijabi a waje, kamar yadda aya ta fadi

- Su dai matan sun ce bassu so ayi musu dole, doka da tun 1979 aka dora musu dole

Zanga-zanga kan hijabi na bazuwa a kasar Farisa ta masu Shi'a
Zanga-zanga kan hijabi na bazuwa a kasar Farisa ta masu Shi'a

A kasar Islama ta Iran, wadda ke karkashin ikon malumai tun bayan juyin juya hali a 1979, shariar Islama ta sanya dole mata a waje su yi lullubi na hijabi, musamman in sun balaga.

A sauran kasashe dai, mata na zanga-zanga ne ta cewa su suna son sanya hijabin. Amma a kasar ta Iran, matan sun ce sam bassu so, wannan dalili na zuwa ne bayan yawancinsu sunyi boko, wasu kuma sun je kasashen turai karatu.

Su dai masu mulki Ustazai sun ki yarda mata su yi yadda suke so da jikinsu, a'a, sun fi so matan suyi aiki da sharia kamar yadda take a Qur'ani, abin da matan ke cewa sun gaji.

DUBA WANNAN: Uwargidan El-Rufai ta wallafa littafi

A watan Disamba ne wata budurwa ta fara wannan kira, inda ta cire hijabin ta a titi ta daure a icce ta yi tutar 'yanci da shi, wadda tuni mahukunta na sharia suka yi awon gaba da ita.

Sai dai hotunan da aka yi ta yada wa a shafukan sada zumunta sun janyo wasu matan suma sun shiiga wannan kirari, da ma a fito da ita, dole aka sako budurwar.

Yanzu dai mata a ko'ina a kasar na ta cire hijabansu suna sanya wa a kan icce, amma kuma ana ganin hukumomi sun fara sassauta musu, gudun kar abinn ya zamo wata babbar tafiya, kamar ta 2009.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng