Abubuwa 5 Da Yakamata Ku Sani Dangane Brice Oligui Nguema, Shugaban Sojojin Juyin Mulkin Gabon
Libreville, Gabon - Ƴan sa'o'i kaɗan bayan hukumar zaɓen ƙasar Gabon a ranar Laraba, ta sanar da cewa Shugaba Ali Bongo ya lashe zaɓe karo na uku, sojoji sun sanar da yin juyin mulki da soke sakamakon zaɓen.
Hakan na zuwa ne bayan ƴan adawa sun bayyana zaɓen a matsayin wanda aka tafka maguɗi a cikinsa.
Mutumin da ake ganin zai maye gurbin Ali Bongo shi ne Brice Oligui Nguema.
Wanene Brice Oligui Nguema?
A cewar rahotanni da dama, Nguema shi ne babban kwamandan dakarun tsaron ƙasar Gabon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1) Nguema: Jiharsu ɗaya da Bongo
Brice Oligui Nguema ɗan asalin Haut-Ogooué ne, inda aka haifi ahalin Bongo.
Bidiyon Halin da Hamɓararren Shugaban Ƙasar Gabon Ke Ciki Ya Bayyana, Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci
Haut-Ogooué shi ne yankin Kudu maso Gabashin ƙasar mafi nisa daga cikin lardunan ƙasar guda tara. An sanya masa suna a dalilin tekun Ogooué. Babban birnin lardin shi ne Franceville.
Ɗaya daga manyan abubuwan da aka fi yi a lardin shi ne haƙar ma'adinai, inda ake samun ma'adinai masu yawa ciki har da zinare.
2) Brice Oligui Nguema: Ɗan uwan Ali Bongo ne
Nguema ɗan uwa ne a wajen Bongo. Rahotanni sun yi yawo cewa shi ne zai maye gurbin hamɓararren shugaban ƙasar.
3) Brice Nguema: Tsohon dogarin mahaifin Ali
Nguema ya riƙe muƙamin ɗaya daga cikin dogaran tsohon shugaban ƙasa Omar Bongo, kafin rasuwarsa a shekarar 2009.
Lokacin da Ali Bongo ya hau kan mulki a watan Oktoba na 2009, an tura Nguema zuwa ƙasashen Morocco da Senegal domin ayyukan diflomasiyya. Shekara 10 bayan nan ya zama shugaban dakarun.
4) Brice Oligui Nguema: Mai goyon bayan tsohon shugaban ƙasar ne
Janar Brice Oligui tsohon mai goyon bayan shugaban ƙasa ne. Yana ɗaya daga cikin mambobin kwamitin CTRI.
Daga cikinsu akwai Kanal ɗin soja da mambobin dakarun tsaro.
5) Brice Oligui Nguema: Hamshaƙin attajiri ne
Bayan ayyukan soji da na diflomasiyya, Nguema hamshaƙin ɗan kasuwa ne wanda ya tara miliyoyin kuɗaɗe.
Nguema an rahoto cewa yana kasuwancin harkokin filaye da gidaje.
Wanene Ali Bongo
Rahoto ya zo cewa sojoji sun hamɓarar da gwamnatin shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo, jim kaɗan bayan an sanar da cewa ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Ali Bongo ya gaji mahaifinsa Omar Bonga a kan kujerar mulkin ƙasar Gabon a shekarar 2009 bayan ya rasu.
Asali: Legit.ng