Shugaban Nijar Ya Bude Baki Ya Yi Magana, Ya Fadi Shekarun da Sojoji Za su Yi a Ofis
- Makonni da karbar mulki da karfin tuwo, Abdourahamane Tchiani ya yi wa ‘Yan Nijar jawabi
- Shugaban gwamnatin sojojin ya yi alkwarin mika mulki ga farar hula cikin shekaru uku masu zuwa
- Janar Tchiani zai fito da sabon kundin tsarin mulki kafin a shirya zabe domin a tsaida shugaba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Niger - Sabon shugaban gwamnatin sojojin Nijar, Abdourahamane Tchiani ya yi wa ‘yan kasarsa jawabi a daren Lahadi.
Aljazeera ta kawo rahoto cewa Janar ya yi magana ga mutanen jamhuriyyar Nijar wanda aka kawo kai-tsaye a talabijin.
A jawabin da ya gabatar, sojan ya bayyana cewa sai nan da shekaru uku za su sauka daga mulki, kwanaki bayan hawansa.
Sojoji sun zauna da ECOWAS a Nijar
Abdourahamane Tchiani wanda ya yi amfani da bindiga wajen samun mulki ya ce za su dawo da farar hula nan da shekaru uku.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan bayani ya fito awanni kadan bayan gwamnatin Tchiani ta zauna da 'yan tawagar ECOWAS da aka tura zuwa Niamey.
Janar Abdulsalami Abubakar (rtd) ne yake jagorantar wannan kwamiti da ake sa ran zai sasanta rikicin shugabancin makwabta.
'Yan Nijar za su samu sabon tsarin mulki
Rahoton ya ce Janar Tchiani ya sha alwashin cewa a cikin wata guda, zai kafa kwamitin da zai duba kundin tsarin mulki.
Wannan kwamiti ne kuma za a ba alhakin fito da sabon tsarin mulkin da gwamnati mai zuwa da Nijarawa za su yi aiki da shi.
Sulhu ko yaki za ayi a Nijar?
Bai da niyyar shiga yaki da kowa, amma idan hakan ya zama dole, sojan ya nuna Nijar za ta yi kokari wajen kare mutuncinta.
Sabon shugaban ya sanar da mutanen Nijar cewa kofa a bude ta ke domin cigaba da yin sulhu, TRK Afrika ta fitar da irin labarin nan.
Babu tabbacin kungiyar ECOWAS za ta amince da hakan musamman da ta ke neman ayi gaggawar dawo da Mohammed Bazoum.
Juyin mulki 4 da aka yi a Nijar
A lokacin da kasashen waje ke neman tsohon shugaban Nijar ya koma kujerarsa, sojoji sun dage kan hukunta Mohamed Bazoum.
Sojojin juyin mulkin Nijar za su tuhumi Bazoum kan zargin cin amanar ƙasa bayan an kifar da gwamnati a karo na hudu a tarihi.
Asali: Legit.ng