Juyin Mulki: Alasanne Ouattara Ya Ayyana Sojojin Nijar a Matsayin 'Yan Ta'adda
- An ayyana sojan da ya yi juyin mulki a Nijar Abdourahmane Tchiani da muƙarrabansa matsayin 'yan ta'adda
- Shugaban ƙasar Kwaddibuwa (Côte d'Ivoire ), Alasanne Ouattara ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis
- Ya ce shirin yaƙin da ECOWAS take ba iya na Najeriya ba ne kaɗai, mataki ne da duka ƙasashen suka ɗauka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban ƙasar Kwaddibuwa (Côte d'Ivoire ), Alasanne Ouattara, ya ayyana sojojin da suka yi juyin mulkin Nijar a matsayin 'yan ta'adda.
Ya bayyana hakan ne a wajen taro na biyu na musamman na ƙasashen ECOWAS, wanda ya gudana a Abuja ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yaƙi da sojojin Nijar ba iya na Najeriya ba ne kaɗai
Ouattara ya bayyana cewa, yaƙin da ake shirin yi domin dawo da dimokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar, ba iya na Najeriya ba ne kaɗai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce duka ƙasashen da ke cikin ECOWAS sun yi amanna da matakin da aka ɗauka, kuma za su ba da cikakkiyar gudummawarsu.
Ya ƙara da cewa an riga da an bi duk wasu matakai na sulhu domin warware matsalar, amma duk ba su yi aiki ba.
Wani ɓangare na kalamansa na cewa:
“Ni ina ganin abinda suka yi a matsayin ta'addanci, saboda haka ba za mu bari hakan ta ci gaba da faruwa ba, za mu ɗauki mataki.”
Kwaddibuwa na goyon bayan ECOWAS
Ouattara ya ce matsayar Kwaddibuwa kan batun a bayyane take, ya ce ƙasarsa ba za ta goyi bayan mulkin soji a ɗaya daga cikin ƙasashen na ECOWAS ba.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi a ce sojojin da suka yi juyin mulkin na can zaune a barikin sojoji ba wai a kan karagar mulki ba.
Ya kuma ce ya fatan za a aiwatar da wannan mataki da ƙasashen na ECOWAS suka ɗauka ba tare da ɓata lokaci ba.
Za mu ɗora alhakin duk abinda Wagner ta yi a kan Rasha
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan gargaɗin da ƙungiyar ECOWAS ta yi wa ƙasar Rasha, a kan dakarun haya na Wagner.
Ta ce za ta ɗora alhakin duk abinda ya faru, na take haƙƙin ɗan adam daga dakarun na Wagner a kan Rasha.
Asali: Legit.ng