Ministan Buhari Ya Ya Ja Kunnen Gwamnatin Tinubu Kan Hambarar da Bazoum a Nijar

Ministan Buhari Ya Ya Ja Kunnen Gwamnatin Tinubu Kan Hambarar da Bazoum a Nijar

  • Abdulrahman Bello Dambazau ya ce kifar da gwamnati da aka yi a Nijar yana da tasiri a Najeriya
  • Tsohon hafsun sojojin kasar ya nuna za a iya fama da matsalar ‘yan gudun hijira idan aka yi sake
  • Janar Dambazau (Mai ritaya) ya ankarar game da halin da ake ciki a Benin, Nijar, Chad da Kamaru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Abdulrahman Bello Dambazau, tsohon soja ne kuma ya rike Ministan harkokin cikin gida, ya yi magana kan rikicin mulkin Nijar.

A makon da ya wuce aka hambarar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyyar Nijar, Janar Abdulrahman Dambazau ya tofa albarkacin bakinsa.

Tsohon shugaban hafsun sojojin ya nuna Najeriya ta na cikin mawuyacin yanayi a halin yau.

Tinubu Bazoum a Nijar
Bola Tinubu a Benin Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Da yake fashin baki a dandalin Twitter, Janar Dambazau mai ritaya ya ce masu tada zaune tsaye sun zagaye kusan duka makwabtan Najeriya.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Yi Amfani da Sojoji a Nijar, A Shiryawa Yaƙi - Sojojin B/Faso da Mali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kasashen Benin, Nijar, Chad da Kamaru su na fama da masu tan tada kayar baya.
Akwai sama da ‘yan gudun hijiran Najeriya 200, 000 sun watsu a kasashen nan. ‘Yan ta’addan ISWAP su na samun damar shiga kasashen nan.
Idan tarzoma ta tashi a Nijar hakan zai iya jawo barkowar ‘yan gudun hijira zuwa Najeriya. Hakan zai jagwalgwala matsalar rashin tsaronmu."

- Abdulrahman Bello Dambazau (Mai ritaya)

Baya ga tsohon Ministan cikin gidan na Najeriya, wasu da-dama su na ta kira ga Bola Tinubu ya guji yin fito na fito da sojojin tawayen da ke Nijar.

Sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula a makwabciyar Najeriya, wasu na ganin idan ECOWAS tayi amfani da karfi, mummunan yaki zai barke.

Idan an ciza, sai a busa!

Aliyu Ibrahim Gebi wanda masani ne a kan harkar tsaro a yankin nan na Afrika, ya dade da yin hasashen abin da yake faruwa a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kwanaki Kadan da Yin Juyin Mulki a Nijar, Bola Tinubu Ya Tafi Biki a Kasar Afrika

Bayanin da Gebi ya yi a Twitter ya nuna Burkina Faso da Mali za su goyi bayan Nijar, sannan Rasha za ta iya taimakawa kasar da kayan abinci.

Ganin haka, ya ba Najeriya shawarar tayi amfani da dattaku wajen magance matsalar, ta aika jakadun da za su zauna a sasanta ta lalama.

Kul aka dauki kayan aiki

Rahoton da mu ka fitar kafin yanzu ya ce Femi Falana ya shawarci Tinubu ka da ya jagoranci ECOWAS wajen yin amfani da ƙarfin soja a Nijar.

Lauyan ya ce amfani da ƙarfin soja wajen dawo da farar hula a Niamey ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Hakan ya jefa kasashe a tsaka mai wuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng