Wani Mummunan Hadarin Mota Ya Ritsa Da Masu Aikin Umrah a Saudiyya

Wani Mummunan Hadarin Mota Ya Ritsa Da Masu Aikin Umrah a Saudiyya

  • Wani mummunan haɗarin mota a ƙasar Saudiyya ya janyo asarar rayukan mutane da dama a ƙasar
  • Mutanen da suka rasu a haɗarin motar Alhazai ne masu aikin Umrah ne a cikin Azumin watan Ramadan
  • Mutane da dama da haɗarin motar ya ritsa da su sun samu raunika sosai a haɗarin da ya auku a yankin Aqaaba Shaar

Saudiyya- Wani mummunan haɗarin mota ya ritsa da Alhazai masu aikin Umrah a ƙasar Saudiyya. Haɗarin yayi muni sosai inda aka samu asarar rayuka da dama.

Sannan kuma a mummunan haɗarin motan, ba rayukan Alhazai masu aikin Umrah kawai aka rasa ba, an samu mutane da dama daga cikin su waɗanda suka samu raunika. Rahoton The Holy Mosques

Umrah
Wani Mummunan Hadarin Mota Ya Ritsa Da Masu Aikin Umrah a Saudiyya Hoto: Twitter/theholymosques
Asali: Twitter

Haɗarin motar ya auku ne lokacin da motar bas ɗin dake ɗauke da masu aikin na Umrah, ta haɗe da wata gada, inda tayi ta tungura-gutsi sannan ta kama da wuta.

Kara karanta wannan

Taron Biki Ya Tarwatse Bayan Amarya Ta Gano Wani Babban Sirrin Ango, Bidiyon Ya Yadu

An samu asarar rayukan aƙalla mutum ashirin a haɗarin motar, yayin da wasu mutum ashirin da tara suka samu raunika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Motar bas ɗin wacce ta ɗaukar masu aikin Hajji ce a lokutan gudanar da Ibadah a ƙasar, tana ɗauke ne da fasinjoji da dama masu gudanar da aikin Umrah cikin watan Azumin Ramadan.

Lamarin ya auku ne a Aqaaba Shaar a cikin gundumar Asir ta ƙasar Saudiyya.

Jami'an kai agajin gaggawa sun garzaya wajen domin bayar da taimako da kuma kashe wutar da ta kama a jikin motar.

Bayan Kwashe Dogon Lokaci Yana Jogorantar Sallah, Shuraim Ya Yi Bankwana Da Limanci A Masallacin Makkah

A wani labarin na daban kuma, Sheikh Shuraim yayi bankwana da limancin masallacin Ka'abah na birnin Makkah cikin ƙasa mai tsarki ta Saudiyya.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Sanda Sun Fallasa Fuskokin Mutane 17 da Aka Kama Lokacin Zaɓe a Nasarawa

Sheikh Saud Ash Shuraim yana ɗaya daga cikin limaman masallacin Ƙa'abah na din-din-din waɗanda ke jagorantar Sallah a masallacin mai tsarki. Sheikh Shuraim ya daina limanci ne duk kuwa da akwai sauran ƙarfi a tattare da shi.

Hukumomi basu bayyana takamaiman dalilin da ya sanya limamin mai shekara 59 a duniya ya dakata da limanci ba a masallacin mai tsarki na Ka'abah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel