Ka Kawo Hujja: ’Yan Sanda Sun Kalubalanci Tsohon Gwamna Matawalle Kan Ya Kawo Hujjar an Masa Satar Motoci

Ka Kawo Hujja: ’Yan Sanda Sun Kalubalanci Tsohon Gwamna Matawalle Kan Ya Kawo Hujjar an Masa Satar Motoci

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana halin da aka jefa ahalinsa bayan da ‘yan sanda suka farmaki gidansa don duba wasu abubuwa
  • Ya ce an sace masa motoci da sauran kayayyakin amfani, wanda hukumar ‘yan sanda ta ce sam ba haka bane, basu dauki komai ba
  • A wani sabon batu, rundunar ‘yan sandan ta ce Matawalle ya kawo hujja idan har yana da yakinin an shiga gidansa an sace masa kayayyaki

Rundunar ‘yan sanda ta kalubalanci tsohon gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da bayyana hujjar an sace masa motoci, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan samamen da aka kai masa a gidajensa da ke Gusau da Maradun, Matawalle ya yi ikirarin cewa an yi masa mummunar sata na kadarorinsa.

'Yan sanda sun kalubalanci tsohon gwamnan Zamfara
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle | Hoto: Leadership
Asali: UGC

Batun da Matawalle ya yiwa ‘yan jarida

Kara karanta wannan

"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, tsohon gwamnan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ban taba ganin irin wannan wauta ba inda za a shiga gidan wani haka siddan ba tare da izini ba kamar muna rayuwa a cikin kasar da ba ta da doka.
“Ina Abuja babu wanda ya gaya mani cewa wata kotu ta ba da wannan umarni ko ta gayyace ni kuma na ki amsa.
“Babban abin bakin ciki shi ne, a gidana na Gusau, an karya duk dakunan matana, hatta hijabi sai da suka kwashe. An dauki har da tukunya duk an saka a mota an tafi da su.”

Babu jituwa tsakanin gwamna mai ci da tsohon gwamna Matawalle

A tun farko, gwamnan jihar Zamfara na yanzu ya zargi Matawalle da sace kadarori da kudaden gwamnati ba gaira babu dalili.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Wannan ya kai ga aka samu rashin jituwa a tsakaninsu, har ta kai ga batun ya je gaban hukumomin da ke bincike a yanzu.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnan da kuma jami’an tsaron da ake kyautata zaton sun shiga gidajensa.

Mun kwato motoci masu tsada 40 a gidan Matawalle, gwamnatin Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kwato tsadaddun motoci har guda 40 daga gidan tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Gwamnatin ta kwato motocin ne bayan ta tura jami'an tsaro zuwa gidajensa da ke a birnin Gusau da Maradum a jihar.

Gwamna Matawalle dai ya sauka a mulki ne bayan kammala wa’adi daya, inda ya sha kaye a zaben 18 ga watan Mayun bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.