Dan Afrika da Ya Tafi Taya Rasha Yaki da Ukraine Ya Rasu, an Dawo da Gawarsa Gasarsu

Dan Afrika da Ya Tafi Taya Rasha Yaki da Ukraine Ya Rasu, an Dawo da Gawarsa Gasarsu

  • Wani matashi dan kasar Zambia ya rasu yayin da yake cikin sojojin Rasha a yakin da suke da Ukraine a kwanakin baya
  • An ruwaito cewa, matashin ya yi zaman magarkama a Rasha kafin daga bisani aka sake shi ya shiga yakin kasar
  • An dawo da gawarsa kasarsu, ya samu tarbar jama'ar kasar da manyan jiga-jigan gwamnatin kasar ta Zambia

Zambia - Gawar wani dan kasar Zambia, Lemekhani Nathan Nyirenda da ya mutu a filin daga garin kare kasar Rasha ta iso Lusaka, babban birnin kasar ta Zambia.

An sauke gawar me a filin jirgin saman Kenneth Kaunada na kasa da kasa a ranar Lahadi, kamar yadda majiyar danginsa, Ian Nzaku Banda ta sanar a cikin wata sanarwa.

Ministan wajen Zambia ya bayyana cewa, gawar marigayin ta samu rakiyar jakadan Zambia na kasa Rasha, Mr Shadreck Luwita kuma ta samu tarbar sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mr. Chembo Mbula da danginsa.

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

An dawo da gawar matashin da ya mutu a filin yakin Rasha da Ukraine
Dan Afrika da Ya Tafi Taya Ukraine Yaki da Rasha Ya Rasu, an Dawo da Gawarsa Gasarsu | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

Matashin mai shekaru 23 an ce yana karatu ne a kasar Rasha, kafin daga bisa gwamnatin kasar ta daure shi a magarkama bisa zargin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ce an sake shi a watan Agusta bayan shafe shekaru biyu a magarkama. Ya rasu a filin daga a watan Satumban bana.

Yadda matashin ya rasu a fagen daga

An sanar da ahalinsa da gwamnatin kasar kan rasuwarsa a watan Nuwamban bana kafin daga bisani a fara shirin dauko shi zuwa kasar, inda ya iso a jiya Lahadi.

Kalli hotunan yadda aka dawo dashi:

An ce kasar ta tura matasa da dalibai zuwa filin daga tare da bayyana musu cewa, ba lallai su iya dawowa ba, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Kasashen duniya sun yi ta cece-kuce tun bayan fitowar wani bidiyo na babban jami'i a kasar ta Rasha da ke bayani kan tsarin kai matasa dalibai da fursunoni bakin daga a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe

Kasar Ukraine a baya ta bayyana bukatar a taya ta yaki da kasar Rasha da ta kai mata hari a farkon shekarar nan.

An kai ruwa rana, ana kuma ci gaba da yaki tsakanin Ukraine da Rasha, lamarin da ya jawo asarar rayuwa da daka.

Kasashen biyu na ci gaba da asarar mutanensu tun bayan fara yakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel