Allah Ya Yi Wa Fafaroma Benedict Rasuwa Yana Da Shekaru 95

Allah Ya Yi Wa Fafaroma Benedict Rasuwa Yana Da Shekaru 95

  • Awanni kadan bayan Fafaroma Francis ya tabbatar da rashin lafiyan Benedict XVI, ya rasu yana da shekara 95
  • Vatican ta sanar da rasuwarsa a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba kwanaki bayan fama da rashin lafiya
  • Fafaroma Benedict XVI ya rasu a gidansa da ke Mater Ecclesiae inda ya koma bayan murabus dinsa a matsayin fafaroma a 2013

Vatican City - Tsohon Fafaroma na Katolika, Benedict XVI ya rasu a gidansa da ke Mater Ecclesiae a birnin Vatican.

Kamar yadda Al-Jazeera ta rahoto, Fafaroman ya rasu a ranar Asabar 31 ga watan Disamba.

Fafaroma Benedict
Allah Ya Yi Wa Fafaroma Benedict Rasuwa Yana Da Shekaru 95. Hoto: Photo: Marco Secchi
Asali: Getty Images

Rasuwarsa na zuwa ne bayan rahotanni da dama da suka fito a kafafen watsa labarai da ke nuna cewa yana fama da rashin lafiya.

Fafaroma Francis wanda ya tabbatar da rashin lafiyarsa ya bukaci mutane su masa addu'a ya samu sauki yayin da ya bayyana cewa rashin lafiyan ya yi 'tsanani'.

Kara karanta wannan

Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benedict ne fafaroma tun Afrilun shekarar 2005 har zuwa lokacin da ya yi murabus a 2013, abin da ya bawa duniya mamaki.

A cewar New York Times, an fatan za a tafi da gawarsa zuwa St Peter's Basillica a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu inda mabiya darikar katolika za su tarbi gawar.

Amma, saboda ya yi murabus daga mukamin fafaroma, ba a tabbatar ko za a yi masa jana'iza irin ta fafaroma wanda ya mutu kan mulki ba.

Fafaroma Benedict XVI ya kafa tarihi a matsayin fafaroma na farko da ya fara yin murabus cikin kimanin shekaru 600.

Dangane da yadda za a yi jana'izarsa, Vatican ta ce nan bada dadewa ba za ta fitar da tsare-tsaren amma ta tabbatar za a kai gawarsa St Peter's Basilica inda 'mabiya darikar katolika za su tarbe shi'.

Kara karanta wannan

Daukar Aiki: Yawan Mutanen Dake Neman Aikin NDLEA Ya Haifar da Matsala a Shafin Yanar Gizon Hukumar

Shin Vatican za ta yi wa Benedict XVI jana'iza irin ta fafaroma, wani masanin tarihi ya yi bayani

A game da yadda za a masa jana'iza, masanin tarihi, Agostino Paravicini Bagliani ya ce Fafaroma Benedict XVI ba shine na farko da ya yi murabus ba.

Ya ce maganan jana'izarsa abu ne mai sarkakiya yayin da ya ce ko bayan murabus dinsa, ya zabi ya cigaba da wasu al'adun fafaroma musamman saka farin kaya.

Yayin da ya bada misali da Fafaroma Celestine V wanda shine fafaroma na farko da ya fara sauka daga mukamin a 1294, ba a masa jana'iza irin da fafaroma ba bayan rasuwarsa a 1296.

Kazalika, Fafaroma Gregory XII wanda shine fafaroma na karshe da ya yi murabus kafin Fafaroma Benedict XVI, ya sauya kansa zuwa cardinal lokacin da ya sauka a 1415.

Bagliani ya ce bayan shekaru biyu Fafaroma Gregory XII ya rasu kuma jana'izar cardinal aka masa ba na fafaroma ba.

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Sa An Gaza Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Babu dan uwana da na ke kusanci da shi kamar Bashir, Dahiru Mangal

A wani rahoton, Dahiru Mangal, yayan marigayi mataimakin shugaba kuma mamallakin kamfanin Max Air, Alh Bashir Mangal, ya ce babu wani dan uwansa da ke da kusanci da shi kamar marigayin.

A hirar da ya yi da Daily Trust, Mangal ya bayyana matsayin kaninsa a wurinsa da dangi, inda ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel