Dahiru Mangal: Babu 'Dan Uwana da Nake da Kusanci Dashi Kamar Marigayi CEO Max Air

Dahiru Mangal: Babu 'Dan Uwana da Nake da Kusanci Dashi Kamar Marigayi CEO Max Air

  • Alhaji Dahiru Mangal, yaya ga marigayi Alhaji Bashir Barau Mangal ya ce babu wani 'dan uwan da yafi kusanci da shi fiye da marigayin
  • Dahiru Mangal, wanda shine shugaban kamfanin Max Air, ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai, inda ya siffanta mutuwarsa a matsayin babban rashi
  • A cewarsa, ni na raine shi, na tarbiyantar da shi, na horar da shi duka da iyayyenmu na da rai a lokacin, amma ni kamar mahaifi nake gare shi

Katsina - Alhaji Dahiru Mangal, yaya ga marigayi mataimakin shugaba kuma ma mallakin kamfanin Max Air, Alhaji Bashir Barau Mangal, ya ce babu daga daya cikin 'yan uwansa da suka fi kusanci kamar marigayin.

Dahiru Mangal
Dahiru Mangal: Babu 'Dan Uwana da Nake da Kusanci Dashi Kamar Marigayi CEO Max Air. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Marigayi Mangal ya kwanta dama ne a safiyar Juma'ar da ta gabata bayan wata takaitacciya jinya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

A zantawar da yayi da Daily Trust, Mangal, wanda shine shugaban Max Air, ya bayyana irin matsayin kaninsa a gunshi, ga dangi da kuma kasuwancinsu, inda ya siffanta mutuwarsa a matsayin babban rashi.

"Maganar gaskiya, Bashir ya taso karkashin kulawata, ya kasance tare dani tun yana karami, duk da iyayenmu suna raye a lokacin, ya kasance karkashin kulawata. Na san dabi'arsa, hali da tarbiyyarsa, saboda haka babu abun da zan iya cewa fiye da Inna Lillahi wa inna ilayhi rajiun (Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Eh, mu 'yan uwa ne uwa daya uba daya, amma ni kamar uba nake gare shi, ni na raine shi, na horar da shi sannan na masa tarbiyya. Na san shi mutum ne mai hakuri, karamci da kyauta."

- A cewar hamshakin mai kudin.

Kara karanta wannan

Ba ka Taba Sarewa Wajen Bani Tsaro ba, Ba a Iya Min Amma Na San kai Na Daban ne, Buhari da Shugaban Dogaran Fadarsa

"Yana da barkwanci da dadin mu'amala. Ya koya abubuwa da dama na zamantakewa da hulda da 'yan adam daga gare ni cikin hakuri da natsuwa har zuwa lokacin da ya tsufa, yayi aure, sannan ya zama magidanci.
"Ya rayu tare da ni, saboda haka ba ni da wani 'dan uwa da nake da kusanci da shi sama da marigayi Bashir. Hakan yasa wannan ya zama babban rashi garemu, amma mu fawwala komai ga Allah, saboda Allah ne ya bamu Bashir kuma shi ne ya amshe shi daga garemu. Addu'armu ita ce Allah ya amshi bakuncinsa gami da bashi masauki a Aljannar Firdausi.
"Haka zalika, muna rokon Allah ya albarki 'ya'yansa. Ya bar yara biyar, biyu mata da uku maza. Matan sun kammala karantunsu kuma sun yi aure, su ma mazan sun kammala karatunsu har matakin digiri na biyu kuma yanzu haka sun girma sun zama mutanen kwarai a cikin al'umma. Muna rokon Allah ya masu albarka. Sannan na ce musu su cigaba da yiwa mahaifinsu addu'a, tare da fatan gamawa da duniya lafiya kamar mahaifinsu."

Kara karanta wannan

Wadanda Ke Zagaye da Buhari Duk an Nada su Ba Don Cancanta ba, Jigon APC

- Ya kara da cewa.

CEO Max Air ya Kwanta dama

A wani labari na daban, Alhaji Bishir Mangal, CEO na kamfanin jiragen sama na Max Air, ya riga mu gidan gaskiya.

Mangal ya rasu a ranar Juma'a. 23 ga watan Disamban 2022 a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel