São Tomé & Príncipe da Jerin Kasashe 7 Mafi Karancin Girma cikin Afrika
- A duk Duniya, Afrika ce nahiya mafi yawan al’umma bayan Asiya, tana da girman kilomita miliyan 30
- Tun a shekarar 2018 akwai mutum fiye da biliyan 1.3 da ke rayuwa a nahiyar da ke dauke da bakin fata
- Duk fadin Afrika, akwai wasu kasashe masu karancin girma, a kan tudu Gambiya ce mafi kankantarsu
A wannan rubutu, mun kawo jerin kasashen Afrika masu karancin girman kasa. The Guardian ta fitar da irin wannan rahoto a shekarun baya.
Su wanene wadannan kasashe?
1. Seychelles
Seychelles, tsibiri ne a gabar Tekun Indiya da Ruwan Somaliya, girman tsibirin bai wuce kilomita 1500 ba. Mazauna kasar kimanin 100, 000 ne.
2. São Tomé and Príncipe
A Afrika kasa ta biyu a kankanta ita ce São Tomé and Príncipe. Kasar mai girman 964 km2 tana kan iyaka da Gabon tana da mutane 201, 800.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
3. Mauritius
Kamar yadda jaridar ta kawo jerin kasashe marasa girma, Mauritius wani tsibiri mai kilomita 2000 a kudu maso gabashin nahiyar shi ne na uku.
4. Comoros
Wani kankanin tsibirin shi ne Comoros a kusa da kasashen Mozambique da Madagascar. Ana lissafi mazauna kasar ba su wuce 800, 000 ba.
5. Cape Verde
Cape Verde kasa ce maras girma kuma maras yawan al’umma (akwai mutane kimanin rabin miliyan). Girman ta bai wuce kilomita square 4000 ba.
6. The Gambia
Kasar Gambiya a yammacin Afrika tana cikin marasa girma a fadin nahiyar da kilomita square 10, 380 kamar yadda Wikipedia suka tabbatar a shafinsu.
Sauran kasashen da ke wannan rukuni su ne:
7. Swaziland (Eswatini)
8. Djibouti
9. Ruwanda
10. Burundi
11. Equatorial Guinea
12. Lesotho
13. Guinea Bissau
14. Togo
15. Sierra Leonne
Najeriya za tayi sabon kudi
Kamar yadda Janar Muhammadu Buhari yayi a 1984, Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yace za a fito da sababbin takardun kudi a shekarar bana.
An samu rahoton yadda tattalin arziki zai motsa a sanadiyyar wannan mataki ta fuskar karyewar Naira a kan Dala da tashin farashin kaya a kasuwa.
Asali: Legit.ng