"Ba A Barin Matan Najeriya A Baya": Hotunan Matan Najeriya Sanye Da Anko Na Jana'izar Sarauniya Ya Kayatar
- Jana'iza Sarauniya Elizabeth ta II na cigaba da daukan hankulan mutane a dandalin sada zumunta
- A baya-bayan nan, hotunan wasu mata yan Najeriya na yawo a dandalin sada zumunta sanye da anko na jana'izar sarauniyar
- Rahotanni sun bayyana cewa tun daga Legas a tura wa matan atamfar zuwa Landan saboda bikin kuma za a ajiye a gidan tarihi na Landan
Landan - Wasu mata yan Najeriya a baya-bayan nan sun wakilci kasar a wurin jana'izar sarauniya Elizabeth II.
Kwararren dan jarida, Dele Momodu, ya wallafa wasu hotuna a dandalin sada zumuna inda ya nuna matan Najeriya sanye da anko a wurin jana'izar Sarauniya Elizabth ta II.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Karin Bayani: An Kama Ƴan Ta'addan Da Suka Sace Mahaifiyar Sanatan APC a Kano Da Kuma Kashe Jami'an Tasaro
Anko da ake kira 'aso-ebi' babban lamari ne a bukukuwa na yan Najeriya, kuma wadannan yan matan sun tabbatar sun yi wakilci Najeriya a Landan.
Dukkansu sun saka anko mai launi daban-daban dauke da hoton sarauniya marigayiya Elizabeth ta II da aka aka a jikinsa.
A rubutun da ya yi tare da hoton, Momodu ya bayyana cewa daga Legas aka tura da atamfar zuwa birnin Lanadan.
Rahotanni sun nuna cewa kafafen watsa labarai na kasashen duniya ciki har da Sky News sun watsa rahoton ankon na yan matan Najeriya.
An kuma bayyana cewa fadar Buckingham ta bukaci a kai atamfar gidan tarihi na Landan.
Ga rubutun da ke tare da hotunan:
"Abin a fara kamar wasu kuma babu wanda ya dauke shi da muhimmanci. An dinka tufafin cikin kwana hudu kuma aka tura daga Legas zuwa Landan kwana daya kafin bikin.
"Ya bazu ko ina, an saka a Sky News kuma fada ta bukaci a kawo a nuna a gidan tarihi na Landan ..."
Ga hotunan a kasa:
Yan Najeriya sun yi martani kan hotunan matan da suka saka ankon a jana'izar sarauniya Elizabeth ta II.
Karanta wasu daga cikin abubuwan da masu amfani da dandalin sada zumunta ke fada a kasa:
Ogundarebola:
"Ya yi kyau sosai."
Margaret_antai:
"Asoebi. Naija !!! Irin wadannan abubuwan masu ban mamaki ne suka sa muka fita daban da wasu."
Thatbeardediboboy:
"Wa ya aike wadannan zuwa jana'iza?"
Bookofkingz:
"Dukkan ku kun shiga tarihi."
Kikiscakesandevents:
"Tabbas ina alfahari da kasa ta."
Ilamendi_ybnl5:
"Ba a barin mu a baya a irin wannan abubuwan."
Ayaba_oluwaseyi:
"Sun yi kyau, Najeriya bata daukan na karshe."
Omotioluwabi:
"Ko ita sarauniyar bata sa anko din ba, Najeriya ta yi."
Dalilin Da Yasa Aka Hana Shugaban Kasar Afirka Mai Karfin Fada A Ji Halartar Jana'izar Sarauniyar Ingila
A wani rahoton, Sarki Charles II ya ki amincewa da bukatar Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabwe na halarton jana'izar Sarauniya Elizabeth II.
A cewar The Punch, Shugaban na Zimbabwe da farko ya nemi a bashi izinin ya halarci jana'izar a wasikar da ya tura wa gaisuwar rasuwar sarauniyar.
Asali: Legit.ng