Dalilin Da Yasa Aka Hana Shugaban Kasar Afirka Mai Karfin Fada A Ji Halartar Jana'izar Sarauniyar Ingila

Dalilin Da Yasa Aka Hana Shugaban Kasar Afirka Mai Karfin Fada A Ji Halartar Jana'izar Sarauniyar Ingila

  • Sarki Charles na III ya yi watsi da bukatar shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, na halarton jana'izar Sarauniya Elizabeth II a ranar Litinin, 19 ga watan Satumba
  • Fadar Buckingham, cikin sanarwa da ta fitar, ta ambaci keta hakkin bil adama a kasar da Mnangagwa ke yi
  • Shugaban kasar, da farko, a sakon ta'aziyya ga Sarki Charles II, ya bukaci a bashi izinin halarton jana'izar

Zimbabwe - Sarki Charles II ya ki amincewa da bukatar Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabwe na halarton jana'izar Sarauniya Elizabeth II.

A cewar The Punch, Shugaban na Zimbabwe da farko ya nemi a bashi izinin ya halarci jana'izar a wasikar da ya tura wa gaisuwar rasuwar sarauniyar.

Emmerson Mnangagwa
Dalilin Da Yasa Aka Hana Shugaban Kasar Afirka Mai Karfin Fada A Ji Halartar Jana'izar Sarauniyar Ingila. UCG
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Yi Magana Da CNN, Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Mnangagwa baya cikin jerin shugabanin kasashen duniya da aka gayyata jana'izar da za a yi a fadar Buckingham.

Me yasa aka ki gayyatar shugaban kasar na Africa zuwa jana'izar Sarauniya Elizabeth II?

Charles III, cikin wata sanarwa da babban jami'ar sadarwa, Miss Jannie Vine, ta fitar ya ce an hana shugaban na Zimbabwe zuwa ne saboda rahotannin keta hakkin bil adama a kasarsa.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

"Mai martaba Sarki Charles na III, ya bukaci in sanar da kai cewa ba za a iya amincewa da bukatar Shugaba Mnangagwa ba saboda ya saba da dokokin Birtaniya da ya shafi shugabannin gwamnatin Zimbabwe da masu alaka da su. Akwai kuma batun rahotannin rashin girmama hakkin bil-adama da aka tabbatar na faruwa a Zimbabwe."

Farfesa Yar Najeriya Da Ta Yi Wa Sarauniyar Ingila Fatar Mummunan Mutuwa Ta Bayyana Ainihin Dalilinta

A wani rahoton, Farfesa Uju Anya ta bayyana dalilin da yasa ta furta marasa dadi game da sarauniyar Ingila, Elizabeth ta II a yayin da ta ke gadon mutuwa.

Kara karanta wannan

Wannan Bai Dace Ba: Gwamnatin Rasha Ta Nuna Baci Rai Kan Rashin Gayyatarta Jana'izar Queen Elizabeth

Farfesan, haifafiyar Najeriya wacce ke nazari a bangaren harsuna da yanayin rayuwar al'umma ta janyo cece-kuce a Twitter kan zolayar sarauniyar ta Ingila.

Tuni dai Twitter ta cire rubutun domin ya saba dokokinta.

Marcie Cipriani, mai gabatar da shirya-shirye a talabijin a Amurka, ta tuntubi Farfesa Anya domin gano dalilin da yasa ta furta maganganun game da sarauniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164