Jerin Sarakuna da Masu Rike Mulkin Duniya da Suka Halarci Jana’izar Karshe Ta Sarauniya Elizabeth II

Jerin Sarakuna da Masu Rike Mulkin Duniya da Suka Halarci Jana’izar Karshe Ta Sarauniya Elizabeth II

Manyan masu rike masarauta a duniya na daga cikin jiga-jigai 2000 da suka halarci jana'izar sarauniya Elizabeth II ta Ingila a Westminster Abbey, jiya Litinin 19 ga watan Satumba.

Bayan sharbar kuka da share hawaye, jama'ar Ingila sun ga gawar sarauniya a juya, kuma daga nan ne suka yi sallama da sarauniyar da mulke su tsawon shekaru 76.

Sarakunan da suka samu halartar jana'izar sarauniya Elizabeth II
Jerin sarakuna da masu rike mulkin duniya da suka halarci jana'izar karshe ta sarauniya Elizabeth II | Hoto: @RoyalFamily
Asali: Twitter

Sai dai, kun san manyan masu sarautar duniya da suka halarci bikin? A kasa mun kawo muku jerinsu kamar haka:

  1. Sarki Harald V na Norway
  2. Yarima Albert II na Monaco
  3. Babban Duke Henri na Luxembourg
  4. Sarki Williem-Alexander na kasar Netherlands
  5. Sarki Phillippe na kasar Belgium
  6. Sarki Felipe VI na kasar Spain
  7. Sarki Carl XVI, Gustaf na kasar Sweden
  8. Sarauniya Margrethe II ta kasar Denmark

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban Najeriya ya fadi alakarsa mai karfi da sarauniya Elizabeth

Wadannan sarakuna da aka jirgi sun halarci jana'izar, kuma da su aka yi kusan komai, inji rahoton BBC.

Hakazalika, sarkin Malaysia Sultan Abdullah Sultan Ahmad Shah da sarauniya Tunku Azizah Amina Maimunah Iskandariyah sun halarta, kuma an gansu a zaune bayan Sarki Abdullah II da sarauniya Ranka ta Jordan.

Haka nan, sarki da sarauniyar Japan ma duk sun halarci wannan biki mai dimbin tarihi.

Duk da haka, akwai masu rike da sarautar duniya da ba a gayyata wannan gagarumin bikin binne sarauniya ba, ciki kuwa harda shugabannin kasashen duniya masu.

Vladimir Putin na kasar Rasha bai halarta ba, kuma akwai yiwuwar hakan na da nasaba da mamayar da ya yiwa Ukraine a watan Fabrairu, lamarin da ya kai sanya wa kasar takunkumi.

Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo

A wani labarin, a yayin da ake ci gaba da jigilar binne sarauniyar Ingila Elizabeth II, tsohon shugaban kasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi wata magana mai daukar hankali.

Kara karanta wannan

Twitter Ta Dau Zafi Bayan Dan Amurka Ya Yi Wa Ministan Buhari Izgili, Ya Kira Shi 'Mr Mugu'

Obansaji ya ce yana alaka da dangantaka mai karfi da sarauniya Elizabeth II, inda yace yana mata fatan alheri kuma yana matukar girmama ta, Daily Trust ta ruwaito.

A wata sanarwa da Obasanjo ya fitar ta hannun hadiminsa, Kehinde Akinyemi, ya ce sarauniya na da halin dattaku da iya zama da mutane, kuma shi kansa yana kyakkyawar dangantaka ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.