Jiya ba yau ba: Jarumi Shah Rukh Khan ya cika shekaru 54 a duniya

Jiya ba yau ba: Jarumi Shah Rukh Khan ya cika shekaru 54 a duniya

Mashahurin jarumin fina-finan India kuma Furodusa a masana'antar Bollywood, Shah Rukh Khan ya cika shekaru 54 a duniya.

Sanannen jarumin mai matsakaicin tsawo, an haifeshi ne a ranar 2 ga watan Nuwamba na shekarar 1965 a babban birin kasar India da ake kira da New Delhi.

Jarumin ya samu karatun farkon rayuwarsa ne a makarantar St. Columba daga nan ya zarce kwalejin Hansraj dake jami'ar Delhi. Shah Rukh Khan ya samu shaidar digirinsa na farko da na biyu ne daga jami'ar Millia Islamia a fannin tsimi da tattali.

Jarumin ya auri Gauri Khan a ranar 25 ga watan Oktoba, 1991. Ubangiji ya albarkaci auren da yara uku, maza biyu (Aryan Khan da AbRam Khan) sai mace daya mai suna Suhana Khan.

DUBA WANNAN: Fallasa: An gano yadda Abba Kyari ya ingiza Buhari ya kwace aikin kaddamar da NLTP

A halin yanzu ya cika shekaru 54 da haihuwa a duniya bayan nasarori da dama da ya samu a sana'arsa. Jarumin ya karbi lambobin yabo tare da jinjinawa hadi da karramawa duk ta bangaren sana'arsa.

A yayin da jarumin ke murnar cika shekaru 54 a duniya, al'umma daga sassa daban-daban na duniya sun tayashi farincikin zagoyawar ranar. Sun bayyana hakan ne ta hanyar mika sakonnin taya shi murna.

Shima jarumin bai yi kasa a guiwa ba wajen mika sakon godiyarsa ga dumbin masoyansa da ke fadin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel