Yi Wa Sarauniya Fatar Mutuwa Mai Radadi Ya Janyo Musayar Maganganu Tsakanin Farfesan Najeriya Da Piers Morgan

Yi Wa Sarauniya Fatar Mutuwa Mai Radadi Ya Janyo Musayar Maganganu Tsakanin Farfesan Najeriya Da Piers Morgan

  • Har yanzu dai ba a dena cece-kuce ba game da fatar mutuwa mai radadi da farfesar Najeriya mai zaune a Amurka, Uju Anya ta yi wa marigayiyar Sarauniya Elizabeth II
  • A wannan karon fitaccen mai gabatar da shiri a talabijin dan Birtaniya, Piers Morgan ne ke musayar maganganu da Farfesa Anya cewa idan ta isa ta zo su yi hira ta sake maimaita abin da ta fada game da sarauniya
  • A bangarenta, Farfesa Anya ta mayar da martani tana mai cewa yana zaginta a fili amma furodusansa na kiranta, inda ta ce ba za ta ciyar da makiyanta abinci ba don haka ba za ta yi hira da shi ba

Twitter - Farfesa Uju Anya, haifafar yan Najeriya mai zama a Amurka na musayar maganganu da mai gabatar da shirye-shirye a talabijin, Piers Morgan, kan kalaman da ta fada game da marigayiya Sarauniya Elizabeth II.

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Maka Mijinta a Kotun Saboda Baya Cin Abincinta

Uju da Morgan
Ana Musayar Maganganu Tsakanin Farfesa Anya Da Piers Morgan Kan Yi Wa Sarauniya Fatar Mutuwa Mai Radadi. Hoto: @UjuAnya.
Asali: Twitter

A ranar Alhamis da ta gabata, Uju ta wallafa wani rubutu a shafinta na Twitter inda ta kira Elizabeth II a matsayin:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sarauniyar kasar da ta sata tare da aikata kisar kare dangi"

Ta yi wannan kalaman ne jim kadan bayan likitocin sarauniya Elizabeth II sun sanar da cewa tana kwance rai a hannun Allah kafin a sanar da rasuwarta.

Kamfanin Twitter ta goge wasu rubutun da Anya ta yi kan cewa sun saba dokokinta har ma daga bisani aka dakatar da ita daga yin rubutu.

Bayan dawowarta Twitter, Anya ta bayyana cewa Morgan yana son ya yi hira da ita amma ba za ta taba bashi damar yin hakan ba.

Ta rubuta cewa:

"Piers Morgan yana kira na 'muguwa, sakarya abar kyama' amma furodusansa yana kira na don mu tattauna. Allah ya kyauta."

Kara karanta wannan

Budurwa Tayi wa Banki Fashi Don ta Samu Kudin Maganin Kansar 'Yar Uwarta

Martanin Morgan ga Anya

Da ya ke martani kan rubutun da ta wallafa a Twitter, Morgan ya ce:

"Tabbas ina son in yi hira da ke. Ina son ki sake gwada maimaitawa a gaba na cewa kina fatan sarauniya ta yi 'mutuwa' mai radadi. 'Amma ina zargin masu mumunan nufi da neman tada zaune tsaye a intanet irin ki ba za su iya yin hakan ba"

Anya ta sake mayar masa da martani tana mai cewa:

"A'a, Piers, kana son ka yi hira da ni saboda tauraruwar ta dade da dena haskawa, kuma kana son amfani da ni don farfadowa. Amma ba zan kyale ka ka yi amfani da ni ba. Kamar yadda na ce, ba na saka abinci a bakin makiya na."

Farfesa Yar Najeriya Da Ta Yi Wa Sarauniyar Ingila Fatar Mummunan Mutuwa Ta Bayyana Ainihin Dalilinta

Tunda farko, Farfesa Uju Anya ta bayyana dalilin da yasa ta furta marasa dadi game da sarauniyar Ingila, Elizabeth ta II a yayin da ta ke gadon mutuwa.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Farfesan, haifafiyar Najeriya wacce ke nazari a bangaren harsuna da yanayin rayuwar al'umma ta janyo cece-kuce a Twitter kan zolayar sarauniyar ta Ingila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel