Matar Aure ta Maka Mijinta a Kotun Saboda Baya Cin Abincinta

Matar Aure ta Maka Mijinta a Kotun Saboda Baya Cin Abincinta

  • Joy Eze malamar makaranta ce wacce ta maka mijinta a gaban kotu kan kin cin abincin da ta dafa da yake yi
  • Ta sanar da kotu cewa mijinta yana zarginta da kokarin saka masa guba kuma ya sanar da 'yan uwansa su tuhumeta idan ya mutu
  • Ta fadi yadda mijinta direban adaidaita sahu yasa 'ya'yanta suka jiya mata baya inda ya sanar da su mahaifiyarsu karuwa ce

Wata malamar makaranta mai suna Joy Eze a ranar Alhamis ta maka mijinta mai suna Nuel Chukwu a gaban wata kotun gargajiya dake Jikwoyi a Abuja kan kin cin abincin da zargin tana son saka masa guba.

Eze wacce ke zama a Jikwoyi dake Abuja ta bayyana wannan zargin a yayin da ta mika bukatar saki a gtaban kotun, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Kotun Abuja
Matar Aure ta Maka Mijinta a Kotun Saboda Baya Cin Abincinta. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Ba zan cigaba da zama a inuwa daya da wannan mutumin ba. Ya daina cin abincina, lokacin da na fuskancesa kan lamarin sai yace ya san shirin da nake na halaka shi.
"Ya sanar da 'yan uwansa cewa idan ya mutu ni ce da hannu a ciki, su tuhume ni."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Tace.

Daily Nigerian ta rahoto cewa, ta sanar da kotun cewa ya sa yaranta sun juya mata baya.

"Mijina yana fadawa yarana miyagun abubuwa a kaina. Ya sanar da su cewa ni karuwa ce. Ya sanar musu cewa kaya da takalman da nake sanyawa duk samarina ne ke siya min."

- Tace.

Ta roki kotun da ta tsinke igiyar aurensu kuma ta bata damar rike yaransu.

Wanda ake karar direban adaidaita sahu ne wanda ya halarci kotun, ya musanta dukkan zargin da ake masa.

Kara karanta wannan

Harin 9/11 Na Amurka: Fasto Adebayo Ya Bayyana Yadda Aka Bincike Shi Saboda Yunkurin Siyan Jirgi

Alkali mai shari'a, Labaran Gusau, ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Satumba domin cigaba.

Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta bukaci kotun shari'a dake zama a Magajin Gari, Kaduna, ta ta tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Alhaji Ali garba Ali saboda tsabar jarabarsa.

Daily Trust ta rahoto, mai karar a ranar laraba ta sanar da kotu cewa Garba na neman jima'i ko a lokutan da take al'adan da lokacin azumin watan Ramadan.

Zainab tace sun yi zaman aure na shekara daya kacal inda ta kara da cewa ta bar gidansa ne saboda wannan lamarin.

Wacce ke karar ta yi bayanin cewa a yayin zamansu, Garba ya saba dawowa gida har da rana a lokutan da take jinin al'ada don ya kwanta da ita, wanda addinin Islama bai aminta da hakan ba.

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel