An Fara Kokari a Majalisa Domin Kawo Dokar da za ta hana a tsaida Musulmi da Musulmi

An Fara Kokari a Majalisa Domin Kawo Dokar da za ta hana a tsaida Musulmi da Musulmi

  • Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa yana kokarin yin garambawul ga dokar zabe
  • Smart Adeyemi zai kawo kudiri wanda zai hana jam’iyya ta ba Musulmi-Musulmi ko Kirista-Kirista takara
  • Sanata Adeyemi zai kirkiro wani sashe a dokar zabe, ko da kudirin ya zama doka, zai soma aiki ne bayan 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja – Sanatan dake wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Smart Adeyemi, ya kawo kudirin da zai hana mabiya addini guda su tsaya takara a jam’iyya daya.

Punch tace idan Sanata Smart Adeyemi yayi nasara, ba zai halatta ga Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista suyi takara a karkashin inuwa daya ba.

Kudirin da Sanata Smart Adeyemi ya nunawa ‘yan jarida a garin Abuja a karshen makon jiya, zai kawo gyara ga sashe na 84 na dokar zaben shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Idan kudirin ya zama doka, zai fara aiki ne bayan zaben shekarar badi. Yanzu haka jam’iyyar APC ta tsaida Musulmi-Musulmi a zaben shugabancin kasa.

Da yake yi wa manema labarai bayani a jiya, Smart Adeyemi yace kwaskwarimar da za ayi wa dokar zaben, ba za ta bari a tsaida Musulmai ko Kirista biyu ba.

Majalisar Dattawa
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan Hoto: @TopeBrown/@NgrSenate
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za ayi garambawul ga doka

“Za ayi wa sashe na 84 na dokar zabe garambawul, ta yadda za a cusa sabon sakin layi na uku da zai ce:
Babu jam’iyyar da za ta tsaida mabiya addini guda a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa da na mataimakin shugaban kasa bayan zaben 2023.”

- Cewar Smart Adeyemi

The Cable ta rahoto Sanatan na APC mai rinjaye yana cewa idan wannan ya samu shiga, zai taimaka nan gaba wajen hana yin abin da zai iya raba kan jama’a.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon Jam’iyya Ya Fadawa Peter Obi Sirri 5 Na Lashe Zaben Shugaban Kasa

‘Dan majalisar yake cewa ya tattauna sosai da mutane da abokan aikinsa da shugabannin majalisar tarayya game da yi wa dokar zabe wannan garambawul.

Tikitin Tinubu da Shettima a 2023

Adeyemi yace kungiyar Kiristoci ta CAN tana da dalilin da za ta ji tsoron tsaida Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shetimma da jam’iyyar APC tayi a 2023.

Amma duk da haka, an rahoto Sanatan na Kogi yana cewa duk da Tinubu da Shettima musulmai ne, yayi imani sune suka fi cancanta su karbi mulki.

NEF tana gefe a zaben badi

Tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da su Rabiu Kwankwaso, an samu rahoto kungiyar NEF ta ki fifita wani ‘Dan takarar shugabancin Najeriya.

Shugaban NEF, Farfesa Ango Abdullahi yace a zaben badi, ‘Yan Arewa ba su da wani ‘Dan takara na musamman, amma ba za su zabi mai raba kan mutane ba.

Kara karanta wannan

Shekarau: Yadda Kwankwaso Yayi Min Kwantan Ɓauna, Ya ci Amanata Daga Bisani

Asali: Legit.ng

Online view pixel