Fannin ilimi: Wata kungiyar agaji ta Saudiyya za ta kafa jami'ar Musulunci a Zamfara

Fannin ilimi: Wata kungiyar agaji ta Saudiyya za ta kafa jami'ar Musulunci a Zamfara

  • Najeriya za ta sake samun karin jami'a yayin da wata kungiyar agaji ta bayyana niyyar gina jami'ar Muslunci a jihar Zamfara
  • Gwamnatin jihar ta Arewa maso Yamma ta yi murna da hada kai da kungiyar domin kara kawo inganci a fannin ilimi
  • Najeriya da Saudiyya kasashe ne masu alaka da juna sosai, inda ake yawan samun mu'amala tsakanin kaashen biyu

Jeddah, kasar Saudiyya - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da bayar da fili domin kafa jami’ar Alkur’ani da Musulunci a jiharsa.

Atta’arif Fil-Islam Charity Organisation, mai hedikwata a Jeddah ta Saudiyya ce za ta kafa jami’ar, kamar yadda kamfanin dillacin Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Zamfara za ta samu jami'a kyauta daga Saudiyya
Fannin ilimi: Wata kungiyar agaji ta Saudiyya za ta kafa jami'ar Musulunci a Zamfara | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Wata sanarwa da gwamnati ta fitar a Gusau a ranar Lahadi ta hannun Nasiru Biyabiki, ta ce Matawalle ya bayyana hakan ne a wajen wani liyafan cin abinci da aka yi a Jeddah ta Saudiyya.

Kara karanta wannan

Saura kwana 2 zaben Osun, Jam’iyya ta sa ‘Dan takarar Gwamna ya janye takara

Rahoton ya kuma ce, gwamna Matawalle ya samu wakilcin kakakin majalisar dokokin jiharsa ne, Nasiru Magarya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wanda ya kafa kungiyar ta agaji kuma limamin Masjidur-Rahma da ke Jeddah, Shekh-Khalid Alhammudy, ya ce jami’ar za ta ciyar da harkar ilimi gaba a jihar da ma Najeriya baki daya.

A cewar Alhammudy:

“Kungiyar ba da agajin tana aiki tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyi da hukumomin gwamnati don samar da cibiyoyin horo da sauran muhimman ayyuka a fadin kasashen Afirka.
"Wadannan wasu tsare-tsare ne na kariya ga al'umma da ke tallafawa kasashe masu tasowa don cimma burinsu."

Malamin addinin ya yi alkawarin ci gaba da yi wa Zamfara da Najeriya addu’a domin samun dauwamamman zaman lafiya da ci gaba a fannin addini da tattalin arziki, rahoton People Gazette.

Za mu jajirce aikin ya tabbata, inji gwamnan Zamfara Matawalle

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Babu wata yarjejeniya tsakanimu da ASUU, inji gwamnatin Buhari

A nasa martanin, gwamna Matawalle ya godewa kungiyar bisa wannan karimcin tare da yin alkwarin jajircewar jihar Zamfara wajen ganin an inganta jami’ar da za a samar.

A kalamansa:

"Yana daga cikin ka'idojinmu yin maraba da duk wani yunkurin ci gaba, musamman wanda ke da tasiri kai tsaye ga jiharmu da kasa baki daya."

A wani labarin, farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, babban malami kuma limamin masallacin Harami na Ka'aba mai tsarki ya ziyarci gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum da yammacin jiya Laraba a gidan gwamnati dake Maiduguri.

Imam Bukhari, wanda shi ne Shugaban tsangayar Nazarin Larabci ga wadanda ba larabawa ba a Jami’ar Ummul Qura da ke Makkah, ya je Maiduguri ne bisa gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, Shugaban Gidauniyar Al-Ansar da ke gina jami’ar mai zaman kanta ta farko a jihar Borno.

Limamin, yayin ganawa da Zulum, ya ce ya gamsu matuka da irin kaurin suna da Borno ta yi da kuma dadadden tarihin ilimin Alkur’ani. Ya lura cewa jihar ta shahara da yawan mahaddata Qur'ani a duk fadin duniya.

Kara karanta wannan

Matawalle ya bukaci da a tsawaita shekarun ritaya na jami'an tsaro zuwa 70

Asali: Legit.ng

Online view pixel