Limamin Ka'aba Ya Ziyarci Zulum, Ya Bayyana Irin Yadda Yake Ji Da Zulum
- Gwamnan jihar Borno ya karbi bakuncin limamin masallacin Ka'aba a fadar gwamnatin jihar
- Limamin ya bayyana gamsuwarsa da yadda gwamnan yake gudanar da gwamnatinsa a jihar
- Gwamna Zulum ya nemi tallafin kasar Saudiyya wajen yaki da munanan ra'ayoyi a fadin jihar
Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, babban malami kuma limamin masallacin Harami na Ka'aba mai tsarki ya ziyarci gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum da yammacin jiya Laraba a gidan gwamnati dake Maiduguri.
Imam Bukhari, wanda shi ne Shugaban tsangayar Nazarin Larabci ga wadanda ba larabawa ba a Jami’ar Ummul Qura da ke Makkah, ya je Maiduguri ne bisa gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, Shugaban Gidauniyar Al-Ansar da ke gina jami’ar mai zaman kanta ta farko a jihar Borno.
Limamin, yayin ganawa da Zulum, ya ce ya gamsu matuka da irin kaurin suna da Borno ta yi da kuma dadadden tarihin ilimin Alkur’ani. Ya lura cewa jihar ta shahara da yawan mahaddata Qur'ani a duk fadin duniya.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Afkawa Bankuna Da Ofishin 'Yan Sanda, Sun Yi Barna Sun Tsere
Dr Dikwa ya fassara jawabin Imam Buhari da cewa: "Farfesa Bukhari ya nuna kaunarka musamman, tare da lura da ayyukanka a cikin shekarun da suka gabata kuma hakika yana farin cikin haduwa da kai da gwamnatinka game da ci gaban da aka samu a karkashin jagorancinka."
Gwamnan Zulum cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na Facebook, ya bayyana jin dadinsa, tare da jaddada alaka mai karfi dake tsakanin jihar Borno da kasar Saudiyya.
Ya kuma nemi tallafi daga Gwamnatin Saudi Arabiya a fagen Koyar da Larabci da Ilimin Addinin Musulunci domin kawar da munanan akidu masu tsattsauran ra'ayi tare da fatan dawo da zaman lafiya a Borno.
Hakazalika gwamnan ya bayyana asalin Kanuri, a cewarsa, Kanuri sun yi hijra ne daga kasashen Larabawa zuwa jihar ta Borno.
KU KARANTA: Dan Ba Kara: Dillalan Albasa 'Yan Arewa Sun Haramta Kai Wa 'Yan Kudu Albasa
A wani labarin, Garba Shehu, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wadanda suka yiwa gwamnan jihar Kano tawaye a baya yanzu haka suna cike da nadama, Daily Nigerian ta ruwaito.
Da yake jawabi a lokacin bude taron shekara ta 2021 na kungiyar Editocin Najeriya ranar Litinin a Kano, Shehu ya ce jihar ta samu ci gaba da yawa, cika alkawura da kuma sulhu a karkashin jagorancin Ganduje.
Ya bayyana cewa 'yan Najeriya na bukatar a basu kwarin gwiwa cewa gwamnatoci a dukkan matakai na aiki kai tsaye don kawo karshen rashin tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.
Asali: Legit.ng