Ekweremadu na hanyar zuwa Turkiyya sayan sabuwar koda muka kwamushe shi, Lauyoyi

Ekweremadu na hanyar zuwa Turkiyya sayan sabuwar koda muka kwamushe shi, Lauyoyi

  • Lauyoyin gwamnatin Ingila sun laburtawa kotu abinda ya auku har jami'ai suka damke Sanata daga Najeriya
  • Gwamnatin Birtaniya ta ce ana zargin Sanatan ne da laifin yunkurin cire kodar wani dan talaka
  • Kotu ta bada umurnin cigaba da garkameshi da matarsa a kurkuku zuwa ranar 7 ga wtaan Yuli

Ingila - Bayanai na cigaba da fitowa game da yadda aka kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, tare da matarsa Beatrice Ekweremadu.

Lauyoyin a kotun majistaren Uxbridge sun bayyana cewa an gurfanar Ike Ekweremadu da matarsa ne a kotu bisa zargin yunkurin cire sashen jikin wani yaro.

Arise TV ta ruwaito Lauyoyin da cewa an damkesu ne a tashar jirgin saman Heathrow yayinda suke hanyarsu ta zuwa birnin Istanbul, kasar Turkiyya.

Kara karanta wannan

An hana matar Ekweremadu ganinsa yayin da yaransu suka bayyana a kotu

A cewar lauyoyin, sun kama hanyar zuwa Turkiyya ne domin sayan wata sabuwar kodar bayan sun gaza amfani da kodar yaron da suka kai Ingila cire masa koda.

Hakazalika sun laburtawa kotu cewa diyar Sanata Ekweremadu ce ke fama da ciwon koda kuma an kwana biyu ana mata wankin koda.

Ekweremadu
Ekweremadu na hanyar zuwa Turkiyya sanyan sabuwar koda muka kwamushe shi, Lauyoyi
Asali: Depositphotos

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu a birnin Landan ta hana Ike Ekweremadu beli, tace a garkameshi a Kurkuku

Kotun a Landan ta hana tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice, beli.

Kotun ta bada umurnin a garkamesu a magarkama, rahoton AriseNews.

Ike Ekweremadu tare da matarsa sun gurfana yau Alhamis gaban kotun majistaren Uxbridge.

Yadda Sanata ya dauki 'Dan shekara 15 a cire masa koda, domin Yarsa ta yi lafiya

Sanata Ike Ekweremadu ya yi ikirarin ya rubutawa ofishin jakadancin Birtaniya takarda a game da dashen kodar da za ayi wa diyarsa.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Ekweremadu ya sanar da kasar Birtaniya tun a watan Disamban 2021 cewa zai dauki nauyin bizar wanda zai bada kodar da za a dasawa Ms Sonia Ekweremadu.

Rahoton da Arise TV ta fitar dazu ya bayyana cewa yaron da tsohon shugaban majalisar dattawan ya kawo ‘dan shekara 15 ne, amma sai ya yi karyar cewa ya kai 21.

'Dan majalisar ya yi wa wannan karamin yaron da bai da wurin zama alkawarin cewa rayuwarsa za ta canza idan aka dace, baya ga takardun karya da aka yi masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel