Ba Sani Ba Sabo: Rago Zai Yi Zaman Gidan Kaso Na Shekara 3 Kan Laifin Tunkurin Wata Mata Da Mika Ta Barzahu

Ba Sani Ba Sabo: Rago Zai Yi Zaman Gidan Kaso Na Shekara 3 Kan Laifin Tunkurin Wata Mata Da Mika Ta Barzahu

  • An yanke wa wani rago hukuncin daurin shekaru uku sakamakon kashe wata mata ta hanyar tunkurinta a kirji da yi mata rauni
  • Masu sarautun gargajiya a yankin sun shiga tsakani sun yi shari'a inda mai ragon zai biya iyalan matan shanu 5 kuma ya basu ragon bayan an sako shi daga dauri
  • Wani dan sanda a Sudan ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar da aka yi da shi a gidan rediyo yana mai cewa a yanzu ragon na hannunsu kuma sun amince da hukuncin da aka yanke

Sudan - An yanke wa wani rago hukuncin daurin shekaru uku a gidan gyaran hali bayan an rahoto cewa ya tunkuri wata mata hakan kuma ya yi sanadin mutuwarta, Daily Star ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammanci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

Ragon ya kai wa Adhieu Chaping, mai shekaru 45 hari, ya tunkure ta a kirji sau da dama kafin daga bisani ta rasu a karshen makon da ya gabata.

Ba Sani Ba Sabo: Rago Zai Yi Zaman Gidan Kaso Na Shekara 3 Kan Laifin Tunkurin Wata Mata Da Mika Ta Barzahu
An Yanke Wa Rago Daurin Shekaru 3 a Gidan Yari Saboda Tunkurin Wata Mata Har Lahira. Hoto: Daily Star.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hukuncin da aka yanke masa, ragon zai shafe shekaru uku a daure a wani barikin sojoji bayan masu sarautun gargajiya a Sudan sun yanke masa hukunci kamar yadda News Week ta rahoto.

Mai ragon ya biya iyalan matar diyya da shanu biyar

Wannan hukuncin na zuwa ne bayan mai ragon ya amince zai biya iyalan mamaciyar diyya da shanu guda biyar.

"Ragon ya kai mata hari ne ta hanyar tunkuyarta a kirji kuma dattijuwar ta mutu nan take," dan sanda ya shaida wa gidan rediyo na Eye da ke Sudan.
"Aikin mu a matsayin yan sanda shine tabbatar da zaman lafiya da raba fada. An kama ragon kuma a halin yanzu yana hannun yan sanda a Maleng Agok Payam."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda zaki ya cizge wa mai kula da shi yatsa, yana tsaka da kokarin birge 'yan mata

Hukumomi sun tabbatar da cewa iyalan mamaciyar sun yarda a basu shanu biyar bayan masu sarautan gargagiya sun shiga tsakani, rahoton Ghanawish.

Mai ragon shine wani Duony Manyang Dhal.

A cewar wani jami'i a unguwar mai suna Paul Adhong Majak, masu ragon yan uwan mamaciyar ne kuma makwabta ne.

Za a mika ragon ga iyalan mamaciyar bayan ya kammala zaman gidan kason

An rahoto cewa za a mika ragon ga iyalan Chaping bayan ya kammala zaman gidan yarin.

Iyalan biyu sun ratabba hannu kan yarjejeniyar amincewa da hakan da yan sanda da mutanen gari a matsayin shaidu.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani rahoton, Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel