Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammaci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammaci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kakkausar martani bayan kisan wata yar arewa da yayanta hudu a jihar Anambra
  • Buhari ya sha alwashin daukar tsatsauran mataki a kan yan awaren IPOB da ke yiwa mutane kisan rashin tausayi a yankin kudu maso gabas
  • Ya kuma gargadi ’yan Najeriya da su guji gaggawar yanke hukunci ko daukar duk wani matakin da zai dada dagula al’amura, inda ya nemi a kyale doka ta yi aikinta

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan rashin imani da ake yiwa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a yankin kudu maso gabas da sauran yankunan kasar.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya gargadi masu aikata ta’asar da su tsammaci mataki mai tsauri daga rundunonin tsaro, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammanci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB
Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammanci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Fadar shugaban kasar ta kuma yi gargadi kan daukar kowanne irin mataki na ramuwar gayya daga kowane bangare na kasar.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike kan sahihanci da gaskiyar hotuna masu tayar da hankali da ake yadawa a kan kisan yar arewa da ake zaton yan awaren IPOB sun yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kuma yi kira ga dukkan jama’a da su guji daukan matakan gaggawa ko yanke hukuncin da ka iya kara dagula lamarin, inda ya bukace su da su bari doka ta yi aiki yadda ya kamata.

Fadar shugaban kasar ta kuma gargadi jama’a kan ci gaba da yada hotunan musamman a kafafen sada zumunta domin su ba masu yunkurin raba kan kasar kunya, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Ina gab da haukacewa: Mijin mata da 'ya'ya 4 da IPOB suka kashe ya magantu

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

A baya mun ji cewa magidancin da ya rasa matarsa mai tsohon ciki da 'ya’ya hudu a jihar Anambra, ya bayyana cewa ya ji kamar ya yi hauka sakamakon tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki.

Tsagerun yan bindiga da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne suka kai farmakin inda suka hallaka mutane 12 ciki harda matar mai tsohon ciki, Harira Jibril da yaranta su hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel