Motoccin Bus 89 Da Aka Yi Amfani Da Su a AFCON Sun Yi Layar Zana
- An nemi motocci 89 cikin wadanda aka yi amfani da su a gasar kwallon kafa ta AFCON an rasa
- Rahotanni sun ce kwamitin shirya gasar ta AFCON a Kamaru ta siyo motocci 90 ne amma a halin yanzu daya kacal ake gani
- Har wa yau, wani rahoton ya ce kawo yanzu akwai wasu ma'aikata da suka yi aiki yayin AFCON din amma ba a biya su hakkinsu ba
Kamaru - Kimanin watanni biyu bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Africa ta AFCON a Kamaru, sabbin motoccin bus 89 da aka yi amfani da su wurin jigilar yan wasa da wasu ma'aikata sunyi batar dabo, rahoton The Punch.
Kwamitin shirya gasar ta siyo motocci bus guda 90 da aka yi amfani da su yayin gasar, amma, a yanzu kwara daya tak aka gani, a cewar L'Anecdote, wata jarida a Kamaru.
Motar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru, ke amfani da ita ne kadai wacce aka gani. An rike shi domin yan wasan na Indomitable Lions za su rika amfani da shi domin wasanni na gida.
Har yanzu akwai wadanda suka yi aiki lokacin AFCON amma ba a biya su ba
Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun fito da ke cewa kawo yanzu gwamnatin Kamaru ba ta riga ta biya wasu ma'aikatan AFCON 2023 ba, ratoton The World News.
Teranga Lions na Senegal ne suka lashe gasar karo ta 33 bayan sun yi galaba a kan Egypt a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Wannan shine karo na biyu da kungiyar ta The Pharaohs suka sha kaye a wasan karshe na gasar AFCON.
Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250
A wani rahoton, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.
Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.
Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.
Asali: Legit.ng