Dakarun Rasha sun hallaka Sojojinmu 137 daga fara yaki inji Shugaban kasar Ukraine

Dakarun Rasha sun hallaka Sojojinmu 137 daga fara yaki inji Shugaban kasar Ukraine

  • Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya bayyana adadin sojojin kasan da ya rasa a jiya
  • Volodymyr Zelensky ya yi jawabi a shafinsa na Facebook, ya ce Rasha ta kashe masu sojoji har 137
  • Shugaban na Ukraine ya bayyana cewa a halin yanzu babu wata kasa da ke shirin taimaka masu

Ukraine - Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce akalla sojojinsa 137 aka hallaka a sakamakon barkowar da sojojin kasar Rasha suka yi masu.

Rahotanni daga jaridu da gidan talabijin na ketare irinsu NBC sun ce daga asubar jiya da sojojin Rasha suka shiga Ukraine zuwa yanzu, an rasa sojoji 137.

Baya ga haka, Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa sojojin kasarsa 316 sun samu rauni a hare-haren.

Volodymyr Zelensky ya bada wannan sanarwa da yake magana a shafinsa na Facebook, inda ya ce sauran kasashen Duniya su na tsoron taimakawa Ukraine.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Dakarun Rasha sun kutsa cikin babban birnin kasar Ukraine, Mutane sun yi takansu

Wa zai kawowa Ukraine agaji?

A cewar shugaban kasar, kasashe duk sun gagara fitowa su marawa sojojin Ukraine baya a yakin.

Dakarun Rasha
Daya daga cikin Sojojin Rasha Hoto: emerging-europe.com
Asali: UGC

Wani ‘dan jarida ya wallafa bidiyon jawabin shugaba Zelensky a shafinsa na Twitter. Ukraniyawa su na ganin kamar kasashen yamma sun juya masu baya yanzu.

Gwamnatin Ukraine ta bakin ma’aikatar tsaron cikin gida ta bada sanarwar cewa ba za ta bar mutanenta masu shekara 18 zuwa 60 su sulale daga kasar ba.

An hana mutane barin Ukraine

“Duk wani namiji mai shekaru daga 18 zuwa 60, bai isa ya bar Ukraine ba. Wannan doka za tayi aiki a lokacin da dokar sojoji ta ke aiki.” - Gwamnati

Kafin nan, The Daily Wire ta rahoto Zelensky yana mai cewa Ukraine za ta ba duk wani wanda yake da niyyar kare kasarsa makami domin a yaki sojojin Rasha.

Kara karanta wannan

Rasha vs Ukraine: Ku Rufa Mana Asiri, Ku Ja Bakinku Ku Yi Shiru, 'Yan Najeriya Sun Shawarci FG

A daidai wannan lokaci sai aka ji shugaban Rasha, Vladimir Putin yana bada sanarwar shiga Ukraine, tare da yin barazana ga kasar Amurka da kungiyar NATO.

Rasha ta shiga Ukraine

Kun ji cewa akwai ‘daliban Najeriya da-dama da suke karatu a jami'o'in Ukraine da sun rasa inda za su shiga bayan yaki ya turnuke tsakanin Rasha da Ukraine.

Mafi yawan kasashe sun dauke ‘ya ‘yansu da ke gabashin Ukraine, ‘Yan Najeriya su na can har yau. Mutanen Najeriya kimanin 5, 000 suke karatu a kasar Turan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel