'Allah baya tare da kai': Wani mutum ya faɗa wa Fafaroma a cikin taron mutane

'Allah baya tare da kai': Wani mutum ya faɗa wa Fafaroma a cikin taron mutane

  • A wani yanayi mai ban mamaki, wani mutum, a Birnin Vatican ya bude baki ya fada wa Fafaroma Francis cewa 'Allah baya tare da shi'
  • Lamarin ya faru ne a dakin taro na Paul VI a yayin da Fafaroma Francis ke yi wa mutane jawabinsa na mako-mako da ya saba yi
  • Mutumin ya rika ihu yana cewa 'Ba a tafiyar da Cocin ta yadda Allah ke so' yayin da jami'an tsaro suka fitar da shi waje, Fafaroma ya yi masa addu'a bayan cewa yana cikin damuwa ne

Birnin Vatican - 'Yan sanda sun yi waje da wani mutum wanda ya nuna cewa babu ruwansa da coci sannan ya datse jawabin da Fafaroma Francis ke yi a Vatican, ranar Laraba, rahoton Channels Television.

'Allah baya tare da kai': Wani mutum ya faɗa wa Fafaroma a cikin taron mutane
Wani mutum ya dubi idon fafaroma ya fada masa cewa 'Allah baya tare da shi'. Hoto: Channels Television
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja

Mutumin da ke tsaya a cikin dakin taron rike da takunkumin fuska a hannunsa yana daga wa sama ya rika maimaitawa cikin harshen turanci yana cewa:

"Cocin ba ya tafiya yadda Allah ya ke so".

Mutumin, wanda kuma ya yi magana da harshen Spaniyawa da Italiya, yana cikin wata yanayi na damuwa inda ya rika rokon fafaroman a bashi dama.

A yayin da 'yan sandan Vatican su biyu suka kama shi za su fita da shi waje, ya rika ihu yana cewa,

"Babu ruwan Allah da kai. Kai ba sarki bane."

Channels Television ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne kusa da karshen jawabin karkashen mako-mako da fafaroma ke yi da mabiya addinin kirista a dakin taro na Paul VI.

Fafaroma Francis ya ce mutumin na cikin damuwa kuma yana bukatar addu'a

Kara karanta wannan

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Ɗaya, Ya Siya Mota Da Babur

Fafaroman, mai shekaru 85, wanda ya cigaba da yin jawabinsa yayin da mutumin ke ihun, ya bukaci al'umma su yi wa mutumin addu'a.

Fafaroman ya ce:

"Mintuna kadan da suka shude, mun ji wani mutum da ke da matsala yana ta ihu, yana kururuwa - ban san ko matsalarsa ta zahiri bane, ko ta kwakwalwa ko kuma aljannu, amma dai daya daga cikin yan uwan mu ne, yana cikin damuwa.
"Ina son na kammala da yi masa addu'a, dan uwan mu yana cikin damuwa. Bawan Allah, yana ihu ne saboda yana cikin damuwa.
"Kada mu manta da dan uwan mu da ke cikin bukata."

Kungiyar Kirista Ta Najeriya Ta Buƙaci Buhari Ya Janye Tallafin Man Fetur Kafin 2023

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kirista ta Najeriya, NCF, gammayar mabiya Katolika da Protestant ta ce ya zama dole gwamnatin tarayyar Najeriya ta jajirce ta ceto kasar daga rushewa ta hanyar cire tallafin man fetur, .

Kara karanta wannan

Jigon Arewa: Laifin 'yan Arewa ne suka sa Jonathan ya gaza karar da Boko Haram

NCF ta ce akwai alamu kwarara da ke nuna cewa idan an cire tallafin man fetur, da aka ce yana lashe kimanin Naira biliyan 250 duk wata, tattalin arzikin zai shiga mummunan hali, Guardian ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a Abuja, shugaban NCF, Bishop John Matthew, tare da sauran shugabannin kungiyar, sun ce tallafin man fetur babban kallubale ne da ya kamata a tunkare shi gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel