Tashin Hankali: Dalibin Sakandire ya zare bindiga, Ya bindige abokinsa ɗalibi a makaranta

Tashin Hankali: Dalibin Sakandire ya zare bindiga, Ya bindige abokinsa ɗalibi a makaranta

  • Wani dalibin babbar Sakandire a ya zare bindiga ya harbe abokin karatunsa ɗalibi bayan wata husuma ta haɗa su
  • Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin ɗan kamanin shekara 16, ya kuma saita bindiga ya kashe kansa baya kashe abokin sa
  • Tuni jami'an yan sanda na ƙasar Afirka ta kudu inda lamarin ya faru, suka fara gudanar da bincike kan musabbabin lamarin

South Africa - Wani ɗalibi dake mataki na 10 ya zare bindiga, ya halaka abokinsa ɗalibi kafin daga bisa ya bindiga kanshi a ƙasar Afirka ta kudu.

Jaridar Eyewitness News ta rahoto cewa hukumar ilimi ta yankin Gauteng ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Laraba, wacce ta kasance rana ta farko a zangon karatu na shekarar 2022.

Afirka ta kudu
Tashin Hankali: Dalibin Sakandire ya zare bindiga, Ya bindige abokinsa ɗalibi a makaranta Hoto: ewn.co.za
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin dan kimanin shekara 16 yana karatu ne a makarantar Lesiba Secondary School dake garin Daveyton.

Kara karanta wannan

Muruwa rigar kowa: Shugaban karamar hukuma ya yanke jiki ya fadi, ya cika a Asibiti

Ɗaliban biyu da lamarin ya faru da su yan aji ɗaya ne, kuma wata yar taƙaddama ce ta haɗa su tun lokacin ɗaukar darasi a makaranta.

Aminiya tace Wannan taƙaddama ce ta sa ɗaya daga cikin su ya zare bindiga ya harbi abokinsa a tsakiyar kai, a wajen harabar makaranta bayan an tashi.

Hakanan, kuma ɗalibin wanda shekarunsa ba su kai ba, ya harbe kansa da bindigar bayan harbin abokin gaddamarsa.

Kakakin sashin ilimi na yankin, Steve Mabona, yace tuni jami'an yan sanda suka fara bincike kan lamarin.

"Jami'an yan sanda suna bincike kan musababbin abin da ya jawo lamarin ya faru. Kuma mun tura jami'an gwajin kwakwalwa domin ɗaukar matakin da ya dace."

Ciyaman ya yanke jiki ya faɗi

A wani labarin na daban kuma Shugaban karamar hukuma ya yanke jiki ya fadi, ya kwanta dama a Asibiti

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya sa ladan tsabar kudi miliyan N5m ga duk wanda ya fallasa yan bindiga a jiharsa

Emmanuel Leweh, ciyaman na ƙaramar hukumar Akwanga, dake jihar Nasarawa, ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan fitowa daga taro.

Mista Leweh, wanda ya kwashe watanni uku kacal a ofishin ciyaman na Akwanga, ya mutu ne a wani Asibitin kuɗi dake babban birnin tarayya Abuja, ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel