Jerin shugabannin Afrika mafi dadewa a kan karagar mulki

Jerin shugabannin Afrika mafi dadewa a kan karagar mulki

Mulki akwai dadi kuma duk yan siyasar da suka dandana shi basa son barin shi cikin sauki. Su kan nemi hanyoyin da za su rike kujerar da karfi ba tare da ya kufce masu ba.

Wannan dabi'a na rike mulki wasu lokutan ba tare da son ran mutane ba ya zama ruwan dare a kasashen Afrika da dama. Nahiyar Afrika ta kasance gidajen shugabanni da dama da suka ki barin kujerar mulki.

Legit.ng ta hada jerin shugabanni mafi dadewa a Afrika.

Jerin shugabannin Afrika mafi dadewa a kan karagar mulki
Jerin shugabannin Afrika mafi dadewa a kan karagar mulki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

1. Shugaba Teodoro Obiang na Equatorial Guinea (shekaru 42)

Shugaba Teodoro Obiang na Equatorial Guinea ne na farko a wannan jeri da daddadun shugabanni. Ya fara zama shugaban kasa a watan Agusta 1979. Ya shugabanci kasar na tsawon shekaru 42.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya hau karagar mulki ta kazamiyar juyin mulkin soji wanda a ciki ya tunkudar da kawunsa Francisco Macías Nguema wanda ya harbe a ranar 29 ga Satumba, 1979.

2. Shugaba Paul Biya na Kamaru (shekaru 39)

Mutum na gaba a wannan jerin shine Paul Biya na Kamaru. Ya hau karagar mulki a 1982 kuma shine shugaban kasar Kamaru bayan shekaru 39. Biya shine na biyu a shugabanni mafi dadewa a Afrika.

3. Shugaba Denis Sassou of DR Congo (shekaru 36)

Denis Sassou ya fara mulkar Dimokradiyyar Congo a matsayin shugaban kasa na tsawon shekaru 12 daga 1979 zuwa 1992 lokacin da Pascal Lissouba ya kayar da shi a zaben shugaban kasa.

Shugaba Denis Sassou ya shirya rundunar da suka yi bore kan Lissouba a 1997, don haka ya sake karbar mulki. Tun daga lokacin yake kan kujerar. An haife shi a 1943, ya shafe tsawon shekaru 36 yana shugabantar kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya dira Maiduguri mintuna bayan harin da Boko Haram ta kai filin jirgi

4. Shugaba Yoweri Museveni of Uganda (shekaru 35)

Yoweri Museveni karbe mulki a matsayin shugaban mulkin soji a shekarar 1986 bayan rundunoni da ke masa biyayya sun fatattaki Milton Obote and Idi Amin.

Shugaban wanda aka haifa a 1944, Museveni ya gyara kundin tsarin mulki don soke wa'adin shugabanci da shekaru. Ya shafe tsawon shekaru 35 yana shugabantar Uganda.

5. King Mswati of Eswatini (shekaru 35)

Har ila yau King Mswati na Eswatini ya shiga jerin. Ya kasance shugaban gidan sarautar Eswatini. An nada tsohon mai shekaru 58 a matsayin sarki a ranar 25 ga watan Afrilu, 1986, yana da shekaru 18.

A matsayinsa na sarki, Mswati ba zai bar kujerar mulkin ba nan kusa. Ya shugabanci masarautarsa tsawon shekaru 36. Sarkin na da mata 16 da yara 36.

6. Shugaba Idris Derby na Chad (shekaru 30)

Shugaba Idris Derby na Chad ma na daya daga cikin shugabannin Afrika da suka dade a mulki. Ya mulki kasar Chadi daga 1990 zuwa 2021 lokacin da yan aware suka kashe shi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanin Dangote, BUA da wasu tallafin kudi N30bn

A matsayinsa na soja, yana jagorantar tawagarsa a filin daga lokacin da aka kashe shi a watan Mayun 2021. Sai dai kuma, dansa Mahamat Deby ne ya gaje shi

7. Shugaba Isaias Afwerky na Eritrea (shekaru 30)

Isaias Afwerky mai shekaru 75 ya shugabanci Eritrea tsawon shekaru 30. Ya fara hawa mulki a 1991 bayan ya kai jam'iyyar Eritrean People's Liberation Front (EPLF) ga nasara. Nasarar da ya yi ta kawo karshen yakin neman ‘yancin kai na shekaru 30 daga Habasha.

Duk da haka ya makale kan mulki tun lokacin. Ana zargin gwamnatinsa da mulkin kama-karya da kuma cin zarafi da dama.

8. Shugaba Ismail Omar na Djibouti (shekaru 22)

An fara zabar Ismail Omar a matsayin shugaban Djibouti a 1999. A lokacin, shine aka fi so ya gaji kawunsa Hassan Gouled Aptidon wanda ya jagoranci Djibouti a matsayin shugaban kasa daga 1977 zuwa 1999.

Daga baya Ismail Omar ya sake lashe zabe a 2005, 2011, 2016 da 2021 a zabukan da 'yan adawa suka kauracewa zaben. Ya shafe shekaru 22 yana mulkin kasar Dibouti.

Kara karanta wannan

Buhari: Sanatoci na kokarin hada-kai domin gyara dokar zabe da karfi da yaji ta Majalisa

9. Sarki Mohammed VI na Morocco (shekaru 22)

Sarki Mohammed na shida ya mulki Morocco tun daga ranar 23 ga Yulin 1999 lokacin da aka nada shi sarauta. Yana cikin daular Alawi mai mulki. Ba zai bar sarauta nan kusa tun shi sarki ne.

Ko da ya yanke shawarar barin kujerar sarautar, dansa kuma mai jiran gado, Moulay Hassan wanda shi ne yarima mai jiran gado zai gaje shi.

10. Shugaba Paul Kagame na Ruwanda (shekaru 21)

Shugaba Paul Kagame ya jagoranci kungiyar Rwandan Patriotic Front, RPF wanda suka sojojin 'yan tawaye da suka taimaka wajen kawo karshen kisan kiyashin da aka yi a Rwanda.

Ya fara zama mataimakin shugaban kasa kuma ministan tsaro Pasteur Bizimungu daga 1994 zuwa 2000.

An zabi Kagame a matsayin shugaban kasa bayan murabus din Bizimungu. An rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a watan Afrilun 2000 kuma tun lokacin ya ke kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

A wani labari na daban, mun ji cewa yayin da shekarar 2023 ke kara gabatowa, 'yan Najeriya da dama sun zuba ido domin ganin wanda zai karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari gabannin babban zabe mai zuwa.

A cikin haka ne babban faston cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya saki hasashensa na abubuwan da za su faru a 2022.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, babban malamin na addinin Kirista, ya ambaci wasu manyan yan siyasa da ka iya zama shugaban kasar Najeriya da mataimakinsa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel