Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zama don kallon jiragen kasa
- Wani matashi dan kasar Birtaniya, Francis Bourgeois, ya bayyana cewa ya yi murabus daga aikinsa domin ya zama cikakken mai kallon jiragen kasa
- Matashin da ke da mabiya sama da 800,000 a Instagram a ko yaushe yakan tsaya kusa da layin dogo yana ihu da jin dadi yayin da jirgin kasa ya wuce
- Jama’a da dama da suka mayar da martani kan lamarin nasa sun bayyana cewa ra’ayinsa mai kyau ne tunda yana sanya farin ciki a fuskokin mabiyansa
Burtaniya - Wani matashi mai suna Francis Bourgeois ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan da ya bayyana a shafukansa na sada zumunta cewa ya bar sana'arsa.
Matashin ya ce yanzu yana so ya yi amfani da cikakken lokacinsa ne kawai don ganin wucewar jiragen kasa. A halin yanzu babu wanda ya san ko zai sami wani aikin a gefe don biyan bukatunsa.
Ya shahara daga aikata wannan lamari
Da ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, matashin ya rubuta cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yau na bar aikina don yin aikin kallon jiragen kasa na cikakken lokaci na!"
A cikin gajeren bidiyon da ya fadi haka, matashin yana murmushi yayin da ya toshe kunnuwansa. Kafar Ladbible ta bayar da rahoton cewa, matashin ya shahara a kasar Birtaniya bayan da ya dauki sha'awar zama mai sana'ar kallon jirgin kasa.
Kalli bidiyon:
Mabiyan sa na kafar sada zumunta
Kullen Korona ne ta ba da gudummawa ga sha'awarsa na barin sana'a ya koma kallon jiragen kasa. Francis yana da mabiya miliyan 1.4 a TikTok da sama da 800,000 a Instagram.
Da yake magana da manema labarai kan sha'awarsa ga sana'ar kallon jirgi ya bayyana cewa:
"A makarantar sakandire, na dan danne sha'awata saboda ba abu ne sananne ba a duniya. Idan na shiga damuwa ko wani abu, lokacin da na ji sautin injuna suna kururuwa, ina jin dadi sosai."
Martanin jama'a
A kasa ga wasu daga cikin martanin jama'a a kafar Instagram:
stephen_brown_1983 ya ce:
"Ya sa ni murmushi sosai, farin ciki sosai. Kyakkyawan saurayi da wasa mai kyau fatan alheri a gare shi."
sampaulsenior5 ya ce:
"Shin ana biyan cikakken ma'aikacin kallon jirgin kasa?"
Pritchardswyd ya ce:
"Yana da kyau. Ina son ganin yadda yake jin dadi lokacin da jirgin ya yi ham. Ra'ayinsa abin ban sha'awa ne."
riskon1 ya ce:
"Madalla da ya sami farin cikinsa."
anoyantunginaka said:
"Ina fatan wani abu mai saukin da zai sa ni farin ciki, ya masa kyau!"
Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka
A wani labarin, wata motar kudi a Amurka ta haifar da wani babban al'amari yayin da daya daga cikin kofofinta ta bude kuma kudade daloli masu yawa suka watse a kasa.
Lamarin da ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, inda ya kawo tsaiko ga cunkoson jama’a a California, yayin da jama’a ke tururuwa domin kwasar rabonsu.
Da take nadar bidiyon lamarin, wata budurwa mai suna Demi Baby a shafin Instagram ta ce wannan shi ne mafi girman abin mamaki da ta taba gani.
Asali: Legit.ng