Yanzu-yanzu: Facebook ya canza suna zuwa Meta, Mark Zuckerberg

Yanzu-yanzu: Facebook ya canza suna zuwa Meta, Mark Zuckerberg

  • Kamfanin Facebook ya sauya sunansa zuwa Meta bayan shekara da shekaru, Mark Zuckerberg ya sanar
  • Kamfanin yace ba zasu canzza sunayen manhajojin kamfanin ba watau - Facebook, WhatsApp da Instagram
  • Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan sauyin suna da kamfanin yayi

Shahrarren Shafin ra'ayi da sada zumunta, Facebook, ya sauya suna zuwa Meta daga ranar Alhamis, 28 ga watam Oktoba, 2021.

Kamfanin ya sanar da hakan a shafinsa misalin karfe 7:45 agogon Najeriya da Nijar.

A jawabin da ya kamfanin yayi, ba za'a canza suna manhajar Facebook, Instagram, Messenger da WhatsApp.

Yace:

"Sanar da Meta - Sabon sunan kamfanin Facebook. Meta zata taimaka wajen gina metaverse, wani waje inda za'a tattauna a 3D. Muna muku maraba zuwa sabon shafin sada zumunta."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da motocci masu bindiga 15 suna can sun kai hari Damboa

"Ba zamu canza sunayen manhajojinmu ba - Facebook, Instagram, Messenger da WhatsApp."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Facebook ya canza suna zuwa Meta
Yanu-yanzu: Facebook ya canza suna zuwa Meta, Mark Zuckerberg Hoto: Meta
Asali: Facebook

Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn

Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da shafukan kamfanin Facebook suka daina aiki, inda ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya.

Zaku tuna cewa shafukan WhatsApp, Facebook, WhatsApp da Messenger sun samu matsala na tsawon sa'o'i bakwai.

Mark Zuckerberg, ya ce bai damu da kudin da ya rasa ba ko kuma yawan masu amfani da suka yi hijira zuwa wasu kafofin sada zumunta yayin da hajojinsa suka daina aiki na tsawon sa'o'i bakwai a ranar Litinin, 4 ga Oktoba.

Zuckerberg, mai kamfanin Facebook wanda ya bayyana matsayinsa a shafin Facebook a ranar Talata, 6 ga Oktoba ya ce ya fi damuwa da wadanda ke dogaro da hajojinsa don cudanya da abokai da dangi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel