Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook
- Wanda ya kirkiri kamfanin Facebook ya bayyana halin da ya shiga yayin da hajarsa ta daina aiki
- Ya bayyana cewa, asarar da ya tafka bata dame shi, kawai mutanen da suka dogara da kafafen ne suka dame shi
- Ya kuma bayyana cewa, masu yada zarge-zarge su daina yada karya cikin al'umma domin ba gaskiya suke fadi ba
California, Amurka - Mark Zuckerberg, ya ce bai damu da kudin da ya rasa ba ko kuma yawan masu amfani da suka yi hijira zuwa wasu kafofin sada zumunta yayin da hajojinsa suka daina aiki na tsawon sa'o'i bakwai a ranar Litinin, 4 ga Oktoba.
Zuckerberg, mai kamfanin Facebook wanda ya bayyana matsayinsa a shafin Facebook a ranar Talata, 6 ga Oktoba ya ce ya fi damuwa da wadanda ke dogaro da hajojinsa don cudanya da abokai da dangi.
Ya rubuta:
"Mun shafe awanni 24 da suka gabata muna bincike kan yadda za mu iya karfafa tsarinmu kan irin wannan gazawar. Wannan kuma tunatarwa ce ga yadda aikin mu yake da mahimmanci ga mutane.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakanan, Zuckerberg ya ce zarge-zargen da ake yada wa na masu satar bayanai kan ayyukan Facebook ba gaskiya ba ne kuma ba su shafi Facebook da 'yan uwanta WhatsApp da Instagram ba.
A kalamansa::
"A zuciyar irin wadannan zarge-zargen shine muna fifita ra'ayin riba akan aminci da walwala. Wannan ba gaskiya bane.”
Karanta cikakkiyar sanarwar cikin harshen turanci:
A rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu, Al Jazeera ta ba da rahoton cewa hadarin da Facebook ya shiga ya nuna illar dogaro da kafafen sada zumunta a matsayin hanya guda ta zamantakewa.
Mutane da dama sun shiga damuwa da rashin amfanin kafafen uku na sada zumunta na tsawon awanni bakwai.
Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi
A baya mun rahoto muku cewa, wanda ya kirkiro kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da dakatar da kafar, inda ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Lamarin da ya janyo asarar ta auku ne cikin sa’o’i kadan kwatsam kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook, Facebook Messenger, Instagram da WhatsApp su ka tsaya cak su ka dena yin aiki.
Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.
Asali: Legit.ng