Sabon kwalbatin da Okorocha ya gina ta bashi kunya
1 - tsawon mintuna
– Ruwa ya shanye sabuwar kwalbatin da gwamna Rochas Okorocha ya gina
– An gina ta ne domin rage cinkoso a kan hanya
– Mabiya hanyar sun soki gwamnati da yin amfani da jabun kayayyaki
Wata sabuwar kwalbatin da gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya gina ta bashi kunya yayinda ambaliyan ruwa ya shanye ta.
KU KARANTA: An yi ma wata mata dukan tsiya a Coci
Anyi kwalbatin a tashan Concorde domin baiwa ruwa daman wucewa domin rage cinkoso akan hanyar mutane.
Amma ,bayan kwanaki biyu da kaddamar da shi, kwalbatin ta zama wata rafi yayinda ruwa ya shanye ta. Mabiya hanyan sun nuna bacin ran su game da gina kwalbatin jabun da aka yi. Sun je anyi ha’inci wajen gina kwalbatin sosai.
Asali: Legit.ng