Yan mata masu kasa da shekara 20 guda 20,000 ke haihuwa ko wace rana
- Kwamitin Majalisar dinkin duniya ta gano yawan mutane ta tabbatr da cewa yan mata masu kasa da shekaru 20 guda 20,000 ke haihuwa a kowace rana a kasashe masu tasowa
- Gwamnatin jihar legas tayi alkawarin zata sa hannun jari cikin ilimantar da yara da karfafa yan mata masu kasa da shekara 20
![Yan mata masu kasa da shekara 20 guda 20,000 ke haihuwa ko wace rana Yan mata masu kasa da shekara 20 guda 20,000 ke haihuwa ko wace rana](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt5ddrc351s4a.jpeg?v=1)
Kwamitin majalisan dinkin duniyan (UNFPA) ta ce yara mata masu shekaru tskanin 15 da 19 guda 20,000 ke haihuwa kulli yaumin a kasashe masu cigaba Yayinda yak e maganan, gwamnatin jihar legas ta bayyana damuwar ta da karuwan zalunci akan ‘yaya mata da kuma kara yawan zubar da ciki. A wata yunkurin kawo sauyi, gwamnatin jihar legas ta sha alwashin sanya hannun jari a karfafa ilimi
Yayinda yake jawabi a taron ranar yawan mutane mai take “ sanya hannun jari cikin yan mata” shugaban ofishin UNFPA na jihar Legas Omoolaso Omosehin yace taken na Magana ne akan yan matan da aka share a al’umma.
KU KARANTA : Boko haram ta kai hari ga jami’an UN a Bama
Game da rahoton Jaridar New Telegraph , mai lakcan ya kara da cewan yan mata masu ciki ya karu a kasha 23 cikin dari
Masu Karin bayani akan zancen , sakataren din din din ma’aikatar tattalin arzikin kasa da kasafin kudi, Abayomi Kadri, yace jihar legas zatayi iyakan kokarinta wajen kawo sauyi cikin al’amarin
Asali: Legit.ng