Najeriya Ta Zama Ƙasa Ta 103 Daga Cikin Kasashen Da Yunwa Ta Yi Wa Katutu a Duniya

Najeriya Ta Zama Ƙasa Ta 103 Daga Cikin Kasashen Da Yunwa Ta Yi Wa Katutu a Duniya

  • Sabon rahoto ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta 103 daga cikin ƙasashe 121 masu yawan mutanen dake fama da yunwa a duniya
  • Wannan na nufin duk da alkawurran gwamnati na yaƙar Talauci, yadda 'yan Najeriya ke kwanciya bacci da yunwa bai ragu ba
  • Shugaba Buhari ya kirkiro shirye-shirye da dama na yaki da talauci amma matsalar tsaro da faɗuwar tattalin arziki sun zama karfen ƙafa

Najeriya ce ƙasa ta 103 daga cikin ƙasashe 121 da ke fama da yunwa a sabon jadawalin yunwa na duniya 2022 da aka fitar.

Sabon rahoton wanda ya fita ranar Jumu'a ya sake bayyana zahirin cewa ƙasar nan na fama da, "matsalar yunwa mai haɗari."

Rahoton ya nuna cewa ƙasashen sun shiga sahun ne bisa la'akari da "Halin tsanani" inda Najeriya ta samu maki 27.3, wanda ke nuna tsananin yunwar da ƙasar ke ciki.

Kara karanta wannan

Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu

Daya daga cikin alkawurran gwamnatin Buhari shi ne yaki da Talauci.
Najeriya Ta Zama Ƙasa Ta 103 Daga Cikin Kasashen Da Yunwa Ta Yi Wa Katutu a Duniya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

PremiumTimes ta ruwaito cewa rahoton na ƙunshe da rukunonin yunwa 5 waɗanda kowace ƙasa ta faɗa ciki - na ƙasa, matsakaici, abun damuwa, mai ban tsoro, da kuma alamar haɗari mafi muni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Najeriya ke tashe a fagen yunwa

Wannan rahoton ya yi kama da na baya kuma babu wani canji da aka samu a kasar nan duk da tsare-tsare fatattakar talauci da gwamnati mai ci ke ikirarin tana yi.

Ƙasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, Najeriya ta kai matsayi na 103 cikin ƙasashe 116 a rahoton 2021 haka kuma itace kasa ta 98 daga cikin 107 a shekarar 2022.

Yunwa na ƙara bunkasa a duniya

A cewar rahoton, wasu mutane Biliyan 828 ne ke fama da yunwa a shekarar 2021, an samu karin mutane biliyan 46 kenan idan aka kwatanta da 2020 da kuma Biliyan 150 tun bayan ɓarkewar Annobar Korona.

Kara karanta wannan

Yadda Zan Tsaya Na Yaki Yan Bindiga Idan Na Zama Shugaban Kasa a 2023, Tinubu

Sahun ƙasashen da yunwa ta fi wa illa ya nuna cewa lamarin ya fi ƙamari a, "Kudancin Afirka dake bakin sahara," da kudancin Asia, babu wani ci gaba da ake samu na kawar da yunwa a waɗannan nahiyoyi.

Sashin rahoton yace:

"Yanayin ka iya ƙara muni duba da yadda rikici ke ƙara yawa a duniya - Sabani, sauyin yanayi, da kuma durkushewar tattalin arziki sakamakon annobar Korona - dukkan waɗan nan direbobi ne dake kara haddasa yunwa."
"Yakin dake wakana a Ukraine ya jawo tashin Farashin Abinci, Man Fetur da Takin Noma kuma zai iya haddasa ƙarancin abinci a 2023 da kuma gaba."

Yadda ake haɗa rahoton yunwa

Rahoton na duba girman alamu hudu ne wajen raba maki ga kowace ƙasa, rashin isasshen Abinci da sauran kayayyaki more rayuwa, wahalar ƙananan yara, watsar da yara da yawan mace-macen su.

Rahoton 2022 ya nuna cewa kaso 12.7 na yan Najeriya ba su samun isasshen Abinci da kayan jin daɗi. Ya kuma nuna cewa kaso 6.5% na yara dake ƙasa da shekaru 5 an yi watsi da su yayin da 31.5% na kananan yara na cikin ƙangin wahala.

Kara karanta wannan

Mazaunin Gidan Haya Ya Sace Mai Gidan Tare da Karɓar Naira Miliyan 1

Bisa la'akari da alamun nan hudu, ana tattara makin ne a kan Sikelin ɗugo 100 wanda ke nuna lamarin ya yi muni. 0 na nuna cewa babu yunwa yayin da maki 100 ne mafi muni.

Jeein kasahen da yunwa ta yi wa katutu fiye da Najeriya

104 Ethiopia

105 Congo

106 Sudan

107 Indiya

108 Zambiya

109 Afghanistan

110 Timor-Leste

111 Guinea Bissau

112 Sierra Leone

113 Lesotho

114 Liberia

115 Jamhuriyar Nijar

116 Haithi, Guinea, Mozambique, Uganda za Zimbabwe

117 Chadi

118 Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Kongo

119 Madagaskar

120 Cetran African Republic

121 Yemen, Burundi da Somalia

A wani labarin kuma mun haɗa muku Jerin Kasashen Duniya 10 Mafi Adadin Rundunar Soja a Duniya a 2022

Wani jerin kasashe masu karfin Soja a duniya a 2022 da Statista ta saki ya nuna cewa kasar Sin ne kan kan gaba wajen yawan jami'an sojoji.

Kara karanta wannan

Mutum 447 Daga Cikin 5,000 Aka Ba Lambar Karramawa Ta Kasa, Minista Ya Yi Bayani Filla-Filla

Rahoton ya nuna cewa kasar sin na adadin Sojoji milyan 2.19 dake shirye da fuskantar yaki. Kasar da ta samu damar zuwa ta biyu itace Indiya mai adadin Sojoji milyan 1.45.

Asali: Legit.ng

Online view pixel