Peter Obi Ya Fadi Gaskiyar Abinda Ya Faru Kan Zargin Kulle El-Rufa'i a Anambra

Peter Obi Ya Fadi Gaskiyar Abinda Ya Faru Kan Zargin Kulle El-Rufa'i a Anambra

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya musanta zargin sanya wa a tsare Gwamna El-Rufai a shekarar 2013
  • Ɗan takarar shugaban kasan yace dukkanin manyan jami'an tsaron da yake tare da su a lokacin yan arewa ne
  • A ranar Litinin, Gwamna El-Rufai ya labarta yadda Obi ya sanya aka tsare shi a Hotel tsawon awanni 48

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ya musanta zargin cewa ya kama tare da garkame gwamna El-Rufai na jihar Kaduna a Anambra lokacin yana matsayin gwamna.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Obi na cewa babu dalilin da zai sa ya ba da umarnin tsare gwamnan domin kwamishinan yan sanda a lokacin ɗan arewa ne.

Gwamna El-Rufai da Peter Obi.
Peter Obi Ya Fadi Gaskiyar Abinda Ya Faru Kan Zargin Kulle El-Rufa'i a Anambra Hoto: Nasiru El-Rufai, Peter Obi
Asali: Facebook

Yace, "Babu hanya ba zan taba yin haka ba. Ban umarci AIG ya kama ko ya tsare wani ba, lokacin ina da Ɗan sandan da babu irinsa a Najeriya, ɗan asalin Kano ne. Kwamishinan yan sanda a lokacin ɗan Adamawa ne."

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

"AIG da aka turo a zaben ɗan jihar Nasarawa ne daga arewa. Ku faɗa mun taya zan amfani da karfi na har na bada umarcin tsare wani, ba ta yadda zan yi haka, ban umarci wani ya yi haka ba a matsayin gwamna."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga ina maganar tsare El-Rufai ta taso?

Idan baku kanta ba, gwamna El-Rufai ya labarta yadda Obi ya sa aka tsare shi lokacin yana kan kujerar gwamnan Anambra a shekarar 2013.

El-Rufai, wanda ya faɗi yadda ta lamarin ya faru a wurin taro da manyan arewa a Kaduna ranar Litinin, ya bayyana cewa Obi ya kama tare da tsare shi na tsawon awanni 48.

A cewar Malam, Peter Obi na fafutukar neman tazarce karkashin inuwar jam'iyyar APGA a wancan lokacin. Yace ya je Anambra ne domin sanya ido kan zaɓen gwamna.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Manyan Arewa a Kaduna, Shugaban Jam'iyya Ya Mutu a Titin Kaduna-Zaria

Yace, "A 2013, na je Anambra a matsayin wakilin jam'iyyar APC da zai sa ido kan zaben gwamna, bakon ku Peter Obi a matsayin gwamna ya sa aka kama ni aka tsare na tsawon awanni 48 a ɗakin Otal."

"Yanzu ni ne gwamnan Kaduna kuma zai zo Kaduna. Kari bayan yan sanda da SSS, ina da rundunar sojoji anan idan ina son kamawa ko tsare wani. Amma mu yan arewa ne mun waye, bama yin haka."

A wani labarin kuma Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

Har yanzun zaman lafiya bai samu matsuguni ba a jam'iyyar PDP duk da kokarin da wasu kusoshi ke yi na kawo karshen rikicin.

A jihar Edo, shugabannin jam'iyyar sun fitar da sanarwan cewa sam ba su yarda da tawagar kamfe ta jihar da suka gani ana yaɗa wa ba.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa mu wayayyu ne: El-Rufai ya tuna yadda Peter Obi ya ci mutuncinsa a 2013 saboda ya je Anambra

Asali: Legit.ng

Online view pixel