Kotu ta bada umarni a daure ‘Dan wasan Bayern a kurkuku saboda tsohon rikici da Budurwarsa

Kotu ta bada umarni a daure ‘Dan wasan Bayern a kurkuku saboda tsohon rikici da Budurwarsa

  • 'Dan wasan Bayern Munchen, Lucas Hernandez yana fuskantar zaman kaso
  • Hernandez ya saba umarnin da Alkali ya ba shi cewa ya rabu da buduwarsa
  • Kotu ta raba Tauraron da sahibarsa ne a sakamakon fada da suka yi tun 2017

Spain – Marca tace tauraron Bayern Munich, Lucas Hernandez zai iya shafe watanni shida a gidan maza saboda saba umarnin da kotu ta yi masa a 2017.

A farkon shekarar 2017 ne jami’an tsaro suka kama ‘dan wasan a sakamakon kwantar da wata budurwarsa da aka yi a asibiti.

Sabani ya shiga tsakanin Lucas Hernandez da sahibarsa a wancan lokaci, har ya ji mata rauni. A dalilin haka sai da Amelia Ossa Llorente tayi jinya a Madrid.

Ganin haka Alkali ya hukunta wadannan mutane biyu, ya hada su da yi wa al’umma aiki na wata guda. Sannan kuma ya hana kowanensu hadu wa da juna.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Bayan abin da ya faru tsakaninsu da hukuncin da Alkali ya yi na cewa Hernandez ya fita harkar budurwar ta sa, sai aka sake ganinsu tare a fili, sun je hutu.

Lucas Hernandez da Amelia Ossa Llorente
Lucas Hernandez da Amelia Ossa Llorente Hoto: www.dailymail.co.uk
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An sake damke Lucas Hernandez

Daga dawowa sai hukuma ta damke ‘dan wasan a filin jirgi. Rahoton yace ba ayi ram da budurwar ba saboda umarnin da kotu tayi a kan ta bai fara aiki ba.

A Disamban 2019 Alkali ya zartar da hukuncin daurin watanni shida a kan Hernandez. A wancan lokaci ‘dan wasan ya na buga kwallo ne a Atletico Madrid.

A ranar Larabar nan, 13 ga watan Oktoba, 2021, wani Alkali a birnin Madrid, kasar Sifen, ya zartar da cewa ‘dan wasan ya saba sharadin da aka sa masa a 2017.

A maimakon ya je kotu, sai aka ji ‘dan wasan mai shekara 25 ya daukaka kara zuwa kotu na gaba.

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

A Sifen, ana afuwa ga wadanda aka yanke wa hukuncin daurin da bai kai shekaru biyu ba, amma ba wannan ne karon farko da aka samu Hernandez da laifi ba.

Thibaut Courtois ya yi baram-barama

A karshen makon da ya wuce ne ‘Dan wasan kwallon kafan da ke tsare ragar kasar Belgium, Thibaut Courtois ya zargi FIFA da UEFA da mugun son kudi.

Courtois yace an fi maida hankali a kan kudin da za a samu, a maimakon lafiya ‘yan wasa. Tauraron ya bayyana haka bayan wasan Belgium da Italiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel