Manchester City, Juventus, Chelsea, da Jerin masu kulobs 7 mafi dukiya a shekarar 2021

Manchester City, Juventus, Chelsea, da Jerin masu kulobs 7 mafi dukiya a shekarar 2021

  • A karshen makon nan aka ji cewa Mike Ashely ya saida kungiyar Newcastle
  • Saudi Arabian Public Investment Fund ta mallaki kungiyar kwallon na Ingila
  • A halin yanzu masu kungiyar Newcastle da Manchester City sun fi kowa kudi

Bayan cinikin Newcastle da aka yi tsakanin Mike Ashely da Saudi Arabian Public Investment Fund, teburin dukiyar kungiyoyin kwallon kafa ya canza.

Africa Sports tace a halin yanzu babu kungiyar da ta kai Newcastle da ke wasa a kasar Ingila arziki.

Wadanda suka mallaki Newcastle sun ba fam Dala biliyan 400 baya. Hakan ya zarce kudin kamfanin Qatar Sports Investment masu kungiyar PSG.

A wani rahoto da The Sun ta fitar, an fahimci cewa Paris Saint-Germain ce ta biyu a jerin, sai Manchester City ta Attajirin balaraben nan Sheikh Mansour.

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Ragowar kungiyoyin da suka cika sahun biyar na farko sune Red Bull Leipzig end Red Bull Salzburg.

Manchester City
Shugabannin Newcastle Hoto: www.skysports.com
Source: UGC

A jerin akwai irinsu mai kungiyar kwallon kafa na Juventus, Andrea Agnelli wanda ake hasashen cewa ya ba fam biliyan £15.7 baya, kusan Naira biliyan 10.

Mai kungiyar Chelsea da ke buga kwallo a gasar Firimiya, Roman Abramovich ya na da £9.6bn, a kudin mu na gida ana hasashen yana da Naira biliyan biyar.

Har ila yau a jerin na shekarar nan akwai Stan Kroenke wanda ya fi kowa hannun jari a Arsenal.

Jaridar ta jero kungiyoyin da masu su, da kuma kudin da suka mallaka:

1. Newcastle – Saudi Arabia Public Investment Fund – £320bn

2. Man City – Sheikh Mansour – £23.3bn

Read also

Wasanni: Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle

3. RB Salzburg, RB Leipzig - Dietrich Mateschitz - £15.7bn

4. Juventus - Andrea Agnelli - £15.7bn

5. Chelsea - Roman Abramovich - £9.6bn

6. LA Galaxy - Philip Anschutz - £8.1bn

7. Arsenal - Stan Kroenke - £6.8bn

8. PSG - Nasser Al-Khelaifi - £6.5bn

9. Inter Milan - Zhang Jindong - £6.2bn

10. Wolves - Guo Guangchang - £5.2bn

A makon nan ne rahotanni su ka zo mana cewa kocin Super Eagles, Gernot Rohr yana bin hukumar kwallon kafan Najeriya albashin watanni takwas.

Duk wata hukumar NFF tana biyan Gernot Rohr da ma’aikatansa Dala $45, 000. (kusan N20m) Matsaloli sun jawo kocin bai samu albashi ba tun Fubrairu.

Source: Legit

Online view pixel