Wani na gida na baiwa yan bindiga bayanai shiyasa aka ki sakin Sarkin Bungudu duk da an biya kudin fansar N20m
- An gano wani na kaiwa yan bindiga bayanai kan Sarkin Bungudu da aka sace
- Iyalan Sarkin sun biya yan bindigan N20m kudin fansa amma basu sakeshi ba
Zamfara - Masu kaiwa yan bindiga bayanai ke hana ruwa gudu wajen yunkurin ceto mai martaba Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru, duk da an biya kudin fansar milyan ashirin.
Yan bindiga sun yi awon gaba da Srkin ne a titin Kaduna-Abuja ranar Talata, 14 ga Satumba, 2021.
Jaridar Punch ta ruwaito hirar da tayi da wani na kusa da iyalan Sarkin wanda ya bayyana cewa akwai wani mai kaiwa yan bindigan bayanai.
Wannan mai kai bayanan ya fadawa yan bindigan cewa su kara neman kudi wajen iyalan Sarkin kuma yana bayyana duk wani tattaunawa da iyalan Sarkin keyi.
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri
Yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Da an saki Sarkin tuni amma akwai mai kai wa yan bindiga bayanai."
"Wannan shine dalilin da yasa yan bindigan ke kara kudin saboda sun san abubuwan da muke tattaunawa."
"Da farko sun bukaci N100m, amma bayan tattaunawa, sun sauko N20m kuma aka biyasu ba tare da bata lokaci ba."
"Abinda ya bamu mamaki shine, yan bindigan sun ce sun samu labarin iyalan Sarki za su iya bayar da ko nawa ne don ceto Sarkin."
Sun ce yanzu N100m za'a biya
Majiyan ya cigaba da cewa yanzu yan bindigan sun ce cinikin ya dawo sabo, N100m za'a biya kudin fansa idan har suna son a saki Sarki.
Yace:
"Kai har fada mana sukayi sun san yadda muka tara N20m din farko. Saboda haka muna cikin wani mugun hali."
An yi kusan kwana 30 da awon-gaba da Sarkin Bungudu, har yanzu babu labarin inda yake
Yanuwa da abokan arziki sun shiga wani yanayi tun bayan da ‘yan bindiga suka dauke Sarkin Bungudu, Mai martaba Hassan Attahiru.
Premium Times tace ana neman a cika wata daya da sace Mai martaba Hassan Attahiru a hanyar Abuja, amma har yanzu jami’an tsaro ba su iya ceto shi ba.
A wata hira da aka yi da Sakataren masarautar Bungudu, Usman Ibrahim ya shaida wa BBC Hausa har yanzu ba su ji wani labari game da Mai martaba ba.
Asali: Legit.ng