An yi kusan kwana 30 da awon-gaba da Sarkin Bungudu, har yanzu babu labarin inda yake

An yi kusan kwana 30 da awon-gaba da Sarkin Bungudu, har yanzu babu labarin inda yake

  • A ranar 14 ga watan Satumba ne aka dauke Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru
  • Tun da aka yi gaba da Sarkin a hanyar zuwa Abuja, har yau ba a fito da shi ba
  • ‘Yan bindiga ba su sake shi ba duk da an tattara masu N20m a matsayin fansa

Zamfara - ‘Yanuwa, talakawa da abokan arziki sun shiga wani yanayi tun bayan da ‘yan bindiga suka dauke Sarkin Bungudu, Mai martaba Hassan Attahiru.

Premium Times tace ana neman a cika wata daya da sace Mai martaba Hassan Attahiru a hanyar Abuja, amma har yanzu jami’an tsaro ba su iya ceto shi ba.

A wata hira da aka yi da Sakataren masarautar Bungudu, Usman Ibrahim ya shaida wa BBC Hausa har yanzu ba su ji wani labari game da Mai martaba ba.

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

“A lokacin da aka dauke shi, mutanenmu da ke wajen jihar suna magana da wadanda suka yi garkuwa da shi. Mun yi tunanin za su fito da shi.”
“Mutanenmu sun fada mana cewa an tabbatar masu da cewa (Sarki) ya na raye.” – Ibrahim.

Alhaji Hassan Attahiru shi ne Sarkin Fulanin Bungudu, kuma ya rike Sakataren gwamnatin jihar Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin Bungudu
Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Me na-kusa da Sarki suke cewa?

Wani na-kusa da Sarkin ya sanar da manema labarai cewa ba su san ko Mai martaban yana raye, ko an kashe shi ba, yace an dai yi masu alkawarin fito da shi.

“Babu wanda ya san ko yana da rai ko ya mutu. Muna sa ran yana raye, amma babu tabbas. ‘Yan bindigan sun fada mana za su fito da shi idan an biya kudi.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako sarkin Bunguda na Zamfara bayan shafe kwanaki a hannunsu

“Mun biya kudin amma ba a ji daga gare su ba tun bayan lokacin da muka kai masu kudin.” – ‘Danuwansa.

A cewar wannan Bawan Allah, tun da aka kai wa ‘yan bindigar kudin fansa, babu wani wanda ya samu damar yin magana da mai martaba saboda rashin waya.

Zuwa yanzu ai an dawo da layukan sadarwa na waya a fadin jihar Zamfara, amma babu wata magana mai karfi da aka ji a kan batun Sarkin na kasar Bungudu.

A farkon makon nan ne aka ji cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta amince da nadin Alkali Muhammad Inuwa Aminu a matsayin sabon Wazirin kasar Zazau.

Sakataren Masarautar Zazzau, Alhaji Barau Musa Aliyu ya aika wa sabon Wazirin takarda zuwa gidansa a Unguwan Juma, a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel