'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Adamawa, sun kuma sace mace mai shayarwa

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Adamawa, sun kuma sace mace mai shayarwa

  • Wasu bata gari da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari ofishin yan sanda a Ngurore
  • Har wa yau, wasu daga cikin bata garin sun kai hari gidan wani Alhaji Umaru sun sace matarsa da 'yarsa
  • Kwamishinan yan sanda na jihar Adamawa ya tura jami'ai na musamman zuwa yankin domin ceto da kama masu laifin

Adamawa - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari caji ofishin yan sanda na Ngurore da ke karamar hukumar Yola ta Kudu inda suka sace mace mai shayarwa a yankin.

A ruwayar The Guardian, DSP Sulaiman Nguroje, mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya tabbatar da kai harin yayin da magana da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Lahadi.

Read also

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Adamawa, sun kuma sace mace mai shayarwa
Masu garkuwa sun kai hari ofishin 'yan sanda a Adamawa. Hoto: Premium Times
Source: Facebook

A cewar Nguroje, gungun bata garin sun kai hari caji ofis din misalin karfe 2 na dare amma babu wanda ya rasa ransa sakamakon harin kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce:

"Wadanda ake zargi masu garkuwar ne sun kai wa wani Alhaji Umaru na Nasarawa B, mazaunin Ngurore a karamar hukumar Yola ta Kudu hari.
"Bata garin sun raba kansu gida biyu; na farko sun kai hari ofishin yan sanda, yayin da sauran kuma suka kia hari gidan Alhaji Umaru, suka sace matarsa, Hauwa Umaru da yar ta."

Kwamishinan 'yan sanda ya tura jami'ai na musamman don ceto

Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Mohammed Barde, ya bada umurnin tura jami'an yan sandan PMF da masu yaki da ta'addanci, CTU da masu yaki da garkuwa da mutane yankin don ceto da kama masu laifin.

Read also

Bayan sa'o'i 4, layukan MTN sun dawo aiki, yan Najeriya sun yi korafi

Nguroje ya ce ana fatan 'yan sandan za su yi bincike tare da wasu masu ruwa da tsaki domin ceto wadanda aka sace da kuma kama bata garin.

Ya ce kwamishinan ya bada tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin aiki da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da doka da oda a Ngurore da wasu sassan jihar.

Daga karshe, ya yi kira ga mutane su cigaba da gudanar da harkokinsu da doka ta hallasta, sannan su kai rahoton duk wani abu da basu amince da shi ba a unguwanninsu zuwa ga jami'an tsaro.

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta fitar da hotunan bindigu da harsasai da ta kwato daga hannun 'yan bindiga a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Yadda waɗanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

Kaduna na daya daga cikin jihohin da 'yan bindiga suka addabi mazaunan jihar ta hari da garkuwa.

ASP Muhammad Jalinge, mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna, wanda ya fitar da hotunan ya kuma ce an bindige wani dan bindiga har lahira yayin musayar wuta da 'yan sanda.

Source: Legit

Online view pixel