Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

  • 'Yan sanda a jihar Kaduna sun yi nasarar damke wasu masu garkuwa da mutane
  • Sun kuma kwato bindigu da dama da harsahi bayan musayar wuta da yan bindigan
  • Har ila yau, yan sandan sun kuma ceto wasu mutane da masu garkuwar suka tsare

Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta fitar da hotunan bindigu da harsasai da ta kwato daga hannun 'yan bindiga a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kaduna na daya daga cikin jihohin da 'yan bindiga suka addabi mazaunan jihar ta hari da garkuwa.

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Dan bindiga da 'yan sanda suka kama a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Dan bindiga da mai yi wa 'yan sanda sojan gona da aka kama a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

ASP Muhammad Jalinge, mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna, wanda ya fitar da hotunan ya kuma ce an bindige wani dan bindiga har lahira yayin musayar wuta da 'yan sanda.

Read also

Yadda waɗanda aka yi garkuwa da su suka shafe kwanaki 53 sun cin ciyawa

Jalinge ya kara da cewa an kuma ceto wasu daga cikin mutanen da yan bindigan suka kama suka yi garkuwa da su.

Har wa yau, ya kuma fitar da hotunan wani dan bindiga da ke karyar cewa shi dan sanda.

Ga hotunan a kasa:

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Bindigu da harsasai da aka kwato hannun 'yan bindiga a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Dan bindiga da ke karyar shi dan sanda ne da aka cafke a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Hotunan muggan bindigu da harsasai da 'yan sanda suka ƙwato daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Dan bindiga tare da makamansa da aka kama shi a Kaduna. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kashe mutum 10, sun raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai Katsina

A wani labari daban, 'yan bindiga a safiyar ranar Talata sun kashe mutum 10 sun kuma raunata wasu da dama yayin sabon harin da suka kai inda suka kona shaguna da gidaje a Yasore, jihar Katsina, mazauna garin suka shaidawa Premium Times.

Yasore ba shi da nisa da Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari.

Batsari na daya daga cikin kananan hukumomin da 'yan bindiga ke yawan kai hari. Yana da iyaka da dajin Rugu, karamar hukumar Katsina da Zurmi a jihar Zamfara.

Source: Legit.ng

Online view pixel